Likitoci sun gano wasu tsutsotsi da ke rayuwa a cikin makogwaron wani yaro mai shekara biyar suna zukar jininsa.
Likitoci sun yi nasarar yi masa tiyatar fitar da tsutsotsi a garinsu na birnin Lincang a Kudancin China kuma.
Yaron ya dade yana fama da ciwo a cikin makogwaronsa da kuma matsalar numfashi sama da shekara daya.
Tsutsotsin suna rayuwa a cikin makogwaron yaron ne inda suke shan jininsa sama da shekara daya.
Bayan rashin samun cikakken nunfashi da yaron ke fama da shi, idan yana barci yakan yi munshari da karfi da daddare.
An samu nasarar gano abin da ke damun yaron ne bayan yi masa tiyata a wani asibiti lokacin da likitan asibitin ya gano ciwon da ke damun sa a makogwaro.
Likitocin asibitin sun zura wasu na’urori a cikin makogwaron yaron daga nan suka ciro wata tsutsa mai tsawon inci 2.8.
Bayan fitar da tsutsar ta nade kamar ba daga cikin makogwaron yaron aka fito da ita ba.
A cewar likitan da ya yi tiyatar akwai alamar cewa tsutsar ta shiga cikin makogwaron yaron ne lokacin da yake shan ruwa mara tsafta ko wanda ba a tace ba, kuma yana kira ga yara da su guji shan ruwa mara tsafta.
Wata kafar labarai a birnin Lincang ta ce abu ne mai wahala a ce tsutsa tana rayuwa har kusan shekara a jikin mutum.
Amma an taba samun rahoton wani yaro mai shekara hudu a yankin a bara wanda aka gano wasu tsutsotsi masu yawa na rayuwa a jikinsa.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta kiyasta cewa, ana iya samun kashi 80 cikin 100 na cututtukan da suka hada da shan inna da amai da gudawa ta hanyar shan ruwa mara tsafta.
Mafi yawan yankunan kasar China ana umartar jama’a su tafasa ruwa kafin su sha.
A watan Afrilu a kasar China an samu rahoton cire wa wani yaro mai shekara tara wata tsutsa mai tsawon inci biyu daga cikin hancinsa bayan shan ruwa mara tsafta a wani yankin karkara.
Likitan ya kara da cewa, jinsin halittun tsutsa suna na iya rayuwa a jikin mutum saboda karfin zukar jini wanda hakan zai taimaka su rayu saboda shan jinin da suke yi.