An kwashi ’yan kallo bayan saukar wani abu da ake zargin kashin tsuntu ne a kafadar Shugaban Kasar Amuka, Joe Biden, a yayin da yake tsaka da gabatar da jawabi.
Ana zargin tsuntsu ya sako wa Mista Biden kashi ne a daidai lokacin da yake jawabi kan sha’anin tattalin arziki da hauhawar farashin kaya a kasar.
- Yadda Sheikh Dahiru Bauchi ya yi bude-baki tare da fastoci
- 2023: Sanatoci na so a ba su takara kai-tsaye
A wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, an ga saukar abin da ake zargin kashin tsuntsu ne a daidai lokacin da Biden ke bayani kan yadda zai rage farashin iskar gas da kuma bunkasa yankunan karkara.
Saukar farin abun a kan rigarsa, daidai kirjinsa ya auku ne a wani kebabben wuri da Shugaba Biden ke kira da “Giant Barn” a cikin Fadar White House.
Sai dai wani ma’aikacin Fadar White House ya ce wasu mutane ne dai ke tunanin haka, amma abin da aka gani ba kashin tsuntsu ba ne.
Duk da haka masu amfani da Twitter sun yi ta yin ba’a da cewa atafau, tsuntsu ne ya sako wa shugaban kashi.
“Kudaje ku rabu da Pence, ai a kafadar Biden tsuntsu ya yi kashi,” inji wani mai sharhi a Twitter, yana shagube kan yadda kudaje suka yi ta yawo a kan tsohon mataimakin shugaban Amurka Mike Pence, a lokacin muhawarsa da Sanata Hillary Clinton.
“Da alama dai ba Biden kadai aka yi wa kashi a yau ba,” inji wani mai tsokaci.
Shi kuma wani cewa ya yi, “Yanzu hatta tsuntsaye abin ya gundure su. Mu je gaba.”
Sai dai da alama duk da abin da ya faru, hakan bai hana Shugaba Biden ci gaba da jawabinsa ba.