✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsoron iyayenmu na hana maza neman aurenmu —’Yan matan barikin soja

Dalilan da ’yan matan barikin soja ke wahalar samun mazan aure

Ana samun bambancin ra’ayi kan abin da ke hana samari zuwa neman auren ’yan mata mazauna barikokin sojoji a Najeriya musamman samarin da ba ’ya’yan sojoji ba ne da su kansu iyayen ’yan matan.

Akwai bayanan da ke nuna cewa samari daga unguwannin da ke kusa da barikokin sojoji a Kaduna suna shakkar shiga cikin barikokin neman ’yan matan wanda hakan ya sa abin ke damun iyayen ’yan matan.

A Jihar Kaduna akwai barikokin soja manya hudu da suka hada da Barikin Soja na 44 da na Ribadu a Unguwar Hayin Banki da na Sojojin Sama da ke Mando da wanda ke Dalet a Unguwar Kawo.

Dukkannin barikokin suna zagaye da unguwannin da ba na sojoji ba ne amma kuma duk da yawan ’yan matan da ke zaune a barikokin tare da iyayensu akasarin samarin da ke kusa da barikokin na shakkar shiga don zantawa da ’yan matan ko da sun ga wadanda suke so da aure.

Iyayen ba su da matsala amma…

Aminu, wani matsashi ne da ya ce ya taba yin budurwa a Barikin Sojoji na 44, inda ya shaida wa Aminiya cewa  ya fuskanci matsala a lokacin da yake zuwa zance a gidan iyayen yarinyar musamman daga wurin ’yan uwanta maza.

A cewarsa, iyayen yarinya maza da mata ba su da matsala da saurayi, idan ya je neman ’yarsu da aure amma yayyen yarinya ko kannenta samari ne ke da matsala.

Ya ce idan har aka ga mahaifin yarinya ya hana saurayi zuwa gidansa sai dai idan ya yi mata miji kuma zai fada wa saurayin ne kai-tsaye ya daina zuwa domin an yi mata miji.

“Gaskiyar lamari shi ne iyayen ’yan mata ba su da matsala da mai zuwa  wurin  ’ya’yansu mata, haka kuma wadansu iyayen maza ba su da matsala.

“Idan iyayen suka gan ka har girmama ka suke yi, kawai abin da ba sa so shi ne ka nemi lalata masu ’ya. Amma idan suka ga da gaske kake yi, to ba ka da matsala.

“Amma idan yarinya na da kanne maza ko yayye maza da suka girma, a nan ne ake samun matsala.

“Sannan akwai kananan sojoji da samarin cikin barikin da kila suna son yarinyar da mutum ke nema.

“Ko da ba da aure suke neman yarinyar ba idan ka fara zuwa sai a nemi a yi maka wulakanci,” inji shi.

“Ya ce suna dukan samari a wani lokaci kuma su tare saurayi su yi masa gargadi da  kada  ya sake  zuwa gidan su  yarinyar.

“Ni dai ba a doke ni ba, amma dai sun gargade ni kan in daina zuwa. Kuma na san wadanda aka yi wa duka daga zuwa zance,” inji shi.

‘Sai ’ya’yanmu sun kammala karatu’

Wata uwa wacce ta kwashe shekaru a Barikin Sojojin Sama na Kaduna, Hajiya Maimuna, ta ce tsoro ke hana samari zuwa cikin barikin neman aure.

A cewarta, ana samun auratayya a tsakanin ’ya’yansu mata da samarin da suka kawo wadanda yawanci daga wajen barikin suka fito.

“Gaskiya sai dai kurum za a iya cewa matasa na tsoron zuwa ne saboda bariki ne. Amma dai wannan ba wata matsala ba ce sosai.

“Zamana a bariki ban fuskanci wannan matsala ba kuma ’ya’yanmu sai sun kammala karatunsu na jami’a wadansu kuma da zarar sun kammala sakandare idan suka samu miji sai su yi aurensu.

“Wata kuma tana cikin jami’a ake daura mata aure sai dai kuma wacce Allah bai kawo mijin da wuri ba sai ta kammala jami’a za ta samu miji.

“Wani abu ne kawai daga Allah ba wai don ba su son yin aure ba ne. Sai dai kurum idan matashi na tsoro ko shakkar wani abu na daban,” inji ta.

Mutanen kwarai muke so —Iyaye

Ta ce ba iyaye ne ke hana auren ’ya’yansu ba, domin samarin ne ke ganin ’yan matan su kuma biyo su gida idan sun daidaita a tsakaninsu sai a yi aure.

Wani limami a daya daga cikin barikokin sojoji da ke Kaduna da bai so a ambaci sunansa saboda ba shi da izinin yin magana da ’yan jarida, ya ce su a matayinsu na iyaye suna bukatar samarin kwarai su auri ’ya’yansu kuma ba sai sojoji ba.

Ya ce magana ce ta aure kuma sojojin an dauko su ne daga jihohin kasar nan daban-daban kuma suna bukatar cudanya da sauran jama’a.

“Abin da muke da bukata shi ne duk inda muka samu kanmu mu ’yan Najeriya ne don haka a dauke mu a hakan.

“Don haka muna bukatar cudanya da al’umma saboda yawancinmu sun zo nan ne sannan muka haifi ’ya’yan kuma ’ya’yan sun girma sannan a can garuruwan  da muka  baro ba su san yaran ba.

“Kuma su ma ’ya’yan ba su san ’yan uwansu da ke garuruwn iyayensu ba.

“Mutanen garin da suke suka sani saboda haka muna bukatar mutanen nan da suka sani su shigo su nemi yaran da aure don mu zama daya,” inji shi.

‘Tsoron cin mutunci’

Game da ko suna samun kukan cewa matasa na tsoron shigowa barikin domin gudun wulakanci sai ya ce: “Gaskiya babu wannan kalubale illa dai iyaka akwai tsoron da mutane ke ji cewa idan sun shigo za a ci mutuncinsu. Amma gaskiya soja ba ya yin haka.

“Kamar yadda lamarin tsaro yake idan ka zo shiga dole ka tsaya a yi maka ’yan tambayoyi domin a san inda za ka, daga nan sai a kyale ka, ka yi tafiyarka ba tare da wulakanci ba.

“Tunda nake ban taba jin an wulakanta wani ba a barikinmu,” inji shi.

Game da ko suna da labarin yayye da kannen ’yan matan na hada baki da kananan sojoji wurin wulakanta samarin da ba ’yan bariki ba sai ya ce: “Gaskiya ban taba jin haka ba.”

‘Za ka ji a jikinka’

Sai dai a cewar Muhammadu Balge da ke zaune a Karar Basi a Jihar Ogun,  mutane da dama na yi wa  auren ’ya’yan soji da ke zaune a bariki kallon sha’ani mai wuya da tsoratarwa, hakan ne ya sa ba su da sha’awar neman aure a barikin soja.

Ya ce bai taba sha’awar auren ’yar soja ba, domin yana ganin hakan ka iya zama hadari ga rayuwarsa.

“A gaskiya ko budurwa ban taba yi a barikin soji ba, domin gudun kada a ba ni kashi.

“Ka san idan ka fara soyayya da ’yar soja iyayenta suka lura ka fara dauke mata hankali ta daina zuwa makaranta to tamkar kana jefa kanka cikin wahala ce, domin in ka je yau ka je gobe wani lokacin in ka je za ka ji a jikinka.

“Musamman idan ka je da wasa ka san gidan soji ba a kai musu wargi, irin ganin yadda suke hukunta masu laifi ne ya sa samari ke taka-tsantsan don kada su shiga hannu.

“Ka san lamarin aure sau tari yana farawa ne kamar da wasa sai ka ga karamar magana ta zama babba, amma tsoron da muke yi wa gidan shi ne ya sa ba a fara wasan balle ya zama gaske,” inji shi.

Ya ce wadansu kuma na ganin in sun auri ’ya’yan sojoji koda sun yi musu laifi ba za su iya ladabtar da su ba, saboda iyayensu.

‘Ban taba samun matsala ba’

Shi kuwa Musa Yahaya Kandi da ke sana’ar shayi a Unguwar Isheri a Jihar Ogun, ya shaida wa Aminiya cewa ya taba yin budurwa a wani barikin soji a Kaduna, kuma bai fuskanci wani kalubale ba, kamar yadda akasarin mutane suke zato.

“Gaskiya mutane na shakkar zuwa barikin soji neman aure domin a tunaninsu in sun yi kure za a hukunta su a ci mutuncinsu a keta musu haddi.

“Wadansu kuma suna ganin ai ’ya’yan barikin sojin ba su da tarbiyya, amma a ganina wannan tunani ba haka ba ne, domin na yi budurwa a Barikin Soji na Jaji lokacin da nake zaune a Kaduna domin ne dan asalin Jihar Jigawa ce.

“A lokacin duk da dai da kuruciyata nakan je mu zauna mu yi hira babu wata matsala, domin muddin ka kiyaye dokokinsu za su karbe ka hannu bibbiyu.

“In za ka shiga ka yi bayani inda za ka ga masu tsaron bariki. Ka fadi lambar gidan da za ka, to ba ka da matsala.

“Haka su ma sojoji suna maraba da masu zuwa neman auren ’ya’yansu, kuma ’ya’yan sojiji akasarinsu suna da tarbiyya domin iyayensu suna sanya ido a kansu, ana ba su horo za ka same su da himma da kwazo da kuma sanin zamantakewa,” inji shi.

Mummunar fahimta aka yi musu

Matashi Muhammed Usman Babawuro da ke zaune a Jihar Legas cewa ya yi ya taba neman aure a barikin soji na Munguno a Jihar Borno, kuma bai fuskanci wata matsala ba, kamar yadda mutane suka dauka.

Ya ce mummunar fahimtar mutanen gari a kan rayuwar mazauna barikin soji na tasiri sosai wajen hana neman ’ya’yan soji da aure kuma hakan na shafar rayuwarsu.

“Musamman a wannan lokaci da ake da marayu da dama cikin ’ya’yan sojin da kuma zaurawa da mazansu suka rasu a fagen fama, lokaci ya yi da za a wayar wa jama’a kai domin su rika mu’amala da su.

“Akwai bukatar a rika zuwa barikoki domin auren ’ya’yan don su ma mutane ne kamar kowa, kuma tarbiyya ko’ina akwai nagari kuma akwai akasin haka,” inji shi.

In za a tuna Aminiya ta taba zantawa da Babban Limamin Masallacin Juma’a na Barikin Dodon da ke Legas, Kanar Sadik Abubakar, wanda a lokacin shi ne Mataimakin Daraktan Harkokin Addinin Musulunci na Rundunar Soji ta 81, kafin ya yi ritaya.

A lokacin ya shaida wa Aminiya cewa fahimtar da wadansu mutanen gari farar hula ke yi game da auren ’ya’yan sojoji mata, cewa auren ’yar soja sai soja ko dan bariki, ba haka ba ne.

“Ina sanar da mutane cewa duk mutumin da yake so ya ga yadda ilimi da tarbiyyar Musulunci suke, to ya shigo bariki.

“’Ya’yanmu suna da ilimin addini da sanin yadda za su zauna da maigida idan sun yi aure.

“Mu ba ma bukatar komai sai sadaki kawai ga duk mutumin da ke bukatar auren ’yarmu.

“Saboda Manzon Allah (SAW) ya ce auren da aka yi da sadaki mai sauki ya fi albarka.

“Saboda haka duk mutumin da ke son auren ’yarmu, kofa a bude take,” inji shi.

Ya ce kada mutum ya ji shakkar zuwa bariki neman auren ’ya’yansu; abin da mutum kawai zai yi, ya tuntubi malaman makarantarsu, su za su hada mutum da iyayen yarinya domin ganin an yi auren cikin tsarin da shari’ar Musulunci ya tanada.

Tsoron iyayenmu ke hana mazan gari neman aurenmu – ’Yan matan barikin soja

Binciken da Aminiya ta gudanar a Barikin Soja na Bukavu da ke Kano ya gano cewa ’yan matan da ke barikin suna daukar lokaci mai tsawo kafin su yi aure inda suka danganta haka da tsoron iyayensu sojoji da mutanen gari suke yi.

Wata budurwa mai suna Fatima ta ce koda sun samu samarin da suke son su, to da zarar sun ji a bariki suke zaune sai su rabu da su.

“Ko ni irin hakan ta faru da ni inda bayan na samu saurayi a waje yana jin wurin da na fito sai ya kama gabansa bai zo ba, irin hakan ya faru da yawa,” inji ta

Rashin mu’amala da mutanen gari matsala ce

Wata budurwa da Aminiya ta tattauna da ita a barikin, mai suna Farida ta ce ba wani abu ke hana su aure ba, illa rashin mu’amala da mutanen gari.

“Ina ganin saboda muna rayuwa a kebance ne, kin san a cikin bariki muna da komai namu, to za ki ga ba mu fiye fita waje sosai ba.

“Amma a yanzu  saboda muna ci gaba da karatu ana samun canji a hankali.

“Za ki ga muna kulla alaka da mutanen gari kuma nan gaba na ina tabbatarwa abin zai canja,” inji ta

A shekarun baya dai Limamin Masallacin Juma’a na Barikin ya yi wata magana a gidan Rediyon Freedom cewa ya kamata mutanen gari su rika shiga cikin barikin suna auren ’ya’yansu lura da cewa ana barin ’yan matan suna girma ba tare da sun yi aure ba.