✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsokaci game da hanyar zuwa Aljanna (9)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin…

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, tare da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa, har zuwa Ranar Sakamako. 

Bayan haka, muna nan dai a kan hanyarmu ta zuwa Aljanna. Mun kwana a kusan rabin karshen tafiyar, wanda ya kunshi barin shirka da sabo, muka kai daidai inda aka ja hankalin kada a yarda a gaskata boka ko mai duba ko mai buga kasa, ya fadi wani abu na ilimin gaibu, alhali ba wanda ya san ilimin gaibu, sai Allah kadai!
Yau ga ci gaba:
5. Kada mu yarda mu yi da’a ga wani sarki ko malami (mai ilimi) ko mahaifi ko mahaifiya ko wani shehi (dattijon gari ko babban malami), a cikin abin da yake na saba wa Allah ne. Idan suka yi umarni da hakan, sai a san yadda za a yi a bayyana musu kin haka din, domin babu biyayya ga kowa wajen halatta abin da Allah Ya haramta ko kuma haramta abin da Ya halatta. Yin haka shirka ne cikin Rububiyyar Allah.
Malam Aljaza’iriy ya ce da wadannan matakai guda biyar da suka gabata, yanzu mun ci rabin hanyarmu. Ba abin da ya rage sai rabin karshe, mun ci kashi uku cikin kashi hudun tafiya. Shi kuwa wannan kashi na karshe shi ne barin sabo (kowane irin sabo), wanda muna magance shi, sai mu isa, mu kai bakin kofar Aljanna. Don haka kada kowa ya tsaya, sai mu tafi mu shige ta, insha’Allah, tare da masu shigarta, muna masu natsuwa, kuma cikin kwanciyar hankali da walwala.
Saboda haka ku taso, ya ku ma’abuta wannan tafiya, kada kowa ya yi kasa a gwiwa, mu dunguma mu tafi gaba daya, kada kowa ya yi jinkiri a kai gaci a bar shi.
Yanzu ga sinadaran karasa tafiya:
1. Mu tsare kwakwalwarmu daga yin tunanin da ba ya da kyau, ba ya da amfani gare mu. Kada mu rika tunanin abin da zai cutar da mu. Lallai mu rika tunani kan abin da shari’a ta gindaya mana, kada mu rika tunani irin na masu amfani da hankalinsu (aklaniyyun), ta yadda duk abin da shari’a ta aje kan wani abu, in bai dace da tunaninsu ba, sai su ki aiki da shi. Wannan tunani ne irin na ’yan tawaye. Kawai idan Allah Ya ce a yi kaza, ko Manzon Allah (SAW) ya ce a yi kaza, to kai a matsayinka na Musulmi, ka bar shi haka nan, ka kama aiki da shi, ka amince, ta yadda ko ba ka gane hikimar da ke cikin abin ba, ka bi kawai, babu shakka, akwai alheri a ciki.
Kada mu rika shirya abin da zai cutar da mutane na barna ko sharri, misali a kashe mutane ko a tunano, a tsara wani tsari da zai sa a rika hallaka al’umma, alhalin ba su san hawa, ba su san sauka ba.
Wato wannan ya nuna mun shiga ‘adabu’ (ladubba) ke nan, bayan mun gitto ‘akidah’ da ‘ibadah’ da ‘akhlaku’!
2. Sannan mu kiyaye jinmu (kunnuwanmu). Lallai mu tsare, mu kiyaye, mu nisanci jin abin da shari’a ta hana, na daga abin da yake karya ko batacce na cutarwa ko alfasha, ko wake-wake na banza. Kade-kade da wake-wake fa suna cikin abubuwan da za su sa a zame daga kan wannan hanya. Ko giba (yi da wani), wato cin naman mutane, ko annamimanci (hada wani da wani don a yi husuma ko tashin hankali ko bata tsakani), ko kaurace wa Musulmi ko a yi wani abu na kafirci.
3. Sannan mu kiyaye ganinmu (idanunmu). Kada mu saki idanunmu mu rika kallon abin da bai halatta mu kalla ba. A rika kallon ‘ajnabiyyai’ (mata ko ’yan mata), a kan titi ne ko talabijin ko jaridu da mujallu, a rika kallonsu tsirara, wannan haram ne, wadda ake kallon Musulma ce ko kafira. Ba ka cewa, ‘Ai ita ta jawo,’ saboda haka sai ka ci gaba da kalla duk haramun ne, wadda ta kame kanta ce ko wadda ba ta kame ba. Kada ka ce ‘Ai ita ba ta kame kanta ba,’ saboda haka ka ci gaba da kallonta, ba daidai ba ne. Ko ita ta wofintar da kanta, kai sai ka kau da kai!
4. Bayan nan, mu tsare harshenmu. Kada mu rika magana ta alfasha, ko mu rika yin batsa, ko mummunar magana, kamar yi wa wani gatse ko dai wata magana mai ban haushi. Ko karya, ko zur (mu fadi abin da ba mu gani ba). Ko yin giba (yi da wani) ko ‘namima’ (hada wani da wani don a saba), duk da harshe ake yin wadannan. Ko kuma zagi ko wata magana mai kama da zagin ko tsinuwa ga wanda bai cancanci a tsine masa ba. Da za ka fita daga wannan mazaunin, ka ga an dauke maka takalmi, kada ka ce ‘Allah Ya tsine wa wanda ya daukar min takalmin nan;’ in ka yi haka, ka zage shi da abin da bai cancanci a zage shi da shi ba. Da sai dai ka ce ‘Allah Ka fitar min da hakkina a kan wanda ya daukar min takalmin nan,’ in ba ka kyale ba ke nan!
5. Sannan mu kiyaye, mu tsare cikinmu, ta yadda kada mu sanya masa abinci ko abin sha da yake haram. Saboda haka kada mu rika cin riba, ko cin mushe, ko cin alade, ko shan duk abin da ke bugarwa ya fitar da mutum daga hayyacinsa, kamar giya (ko abin da ya yi kama da ita na daga abubuwa masu bugarwa). Kada mu sha taba sigari kowace iri. Duk wadannan suna lalata mutum su sanya masa cuta ko wata illa ga rayuwarsa. Ko ba komai ma, illa ta mutunci ai ba karamar aba ba ce. Musamman matasa, su daina shaye-shaye iri-iri, wadanda ke sa su rasa hankalinsu, har su kai ga haukacewa gaba daya. Mutum ya bata rayuwarsa, ya je gidan dawwama ba ya da komai!
6. Bayan nan, mu tsare farjojinmu, mazanmu da matanmu, kada a rika yin zina. Kada mutum ya kusanci wata matar da ba tasa ta shari’a ba ko baiwa, wadda Allah Ya ce ba komai, wadannan a kusance su.
Mu kwana nan!