Allah Ya yi wa Shugaban mabiya ɗarikar Katolika na duniya, Fafaroma Frasncis, rasuwa yana da shekaru 88 a duniya.
Fadar Vatican ce ta sanar cewa da misalin ƙarfe 7.35 Agogon Vatican ne Fafaroma Francis, wanda sunansa na asali Cardinal Jorge Mario Bergoglio, ya rasu a safiyar Litinin a yayin da al’ummar Kirista na duniya ke bikin Ista.
Ya mutu ne washegari da ya fito bainar jama’a a Dandalin St Peter’s, domin taya Kiristoci murnar zagayowar ranar Ista.
Fafaroma Francis ya yi fama da doguwar jinya, inda a watan da ya gabata ne aka sallame daga asibiti bayan ya shafe makonni biyar can sakamakon cutar sanyin haƙarƙari mai tsanani.
A shekarar 2023 ne aka naɗa marigayin a matsayin Fafaroma bayan Fafaroma Benedict XVI ya yi ritaya. Benedict XVI shi ne fafaroma na farko da ya yi ritaya daga muƙamin don ƙashin kansa a tsawon shekaru 600.
Fafaroma Francis wanda ake wa kallon mai sassaucin ra’ayi kuma ya yi ƙoƙarin ra’ayin cocin game da auren jinsi da sakin aure. Hakazalika ya yi kokarin ganawa da jagororin wasu addinai.
A zamanin shuagabancin Fafaroma Francis, zargin limaman coci da lalata ƙananan yara ya dabaibaye Cocin Katolika, inda ya buƙaci a ɗauki ƙwararan matakai domin hana rufa-rufa kan lamarin. Amma duk da haka wasu na zargin sa da rashin yin abin da ya kamata wajen tabbatar da ganin an hukunta jagoranrom da suka ki miƙa rahoton malaman da ake samu da laifin cin zarafin.
Fafaroma Francis shi ne na farko daga nahiyar Amurka, kuma na farko daga yankin Kudancin duniya.
Rabon da a samu fafaroma ba daga nahiyar Turai ba tun kafin kafin mutuwar Fafaroma Gregory III wanda aka haifa a ƙasar Syria a shekarar 741.