✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama tsohuwa kan zargin lalata da almajiri a Bauchi

Ana zargi Baba Mai Ɗan Wake da laifin yin fasikanci ta hanyar tilasawa da yaudara da wani almajiri ɗan kimanin shekaru 14 ya yi lalata…

Hukumar Hisbah ta kama wata mata mai sana’ar ɗan wake kan zargin ta da yin lalata da wani almajiri dan shekara 14 a garin Azare da ke Jihar Bauchi.

Shugaban Hukumar ta Hisbah na shiyyar Katagum da ke Azare, Malam Ridwan Muhammad  Khairan ya bayyana cewar, ana zargin matar, wadda ake kira Baba Mai Ɗan Wake da laifin yin fasikanci ta hanyar tilasawa da yaudara da wani almajiri dan kimanin shekaru 14, bayan ta sanya masa maganin ƙarfin maza a cikin lemon kwalba don ya riƙa biya mata buƙata.

Ya ce almajirin ya haɗu da Nana Mai Ɗan Wake da yake mata wanke-wanke a Sabuwar Tashar Jama’are ne, a cikin garin Azare, inda ta buƙaci ya riƙa zuwa gidanta yana kwana, inda ta rika yaudarar sa har ta riƙa yin lalata da shi.

A cewar Malam Ridwan Mohammed Khairan, sun cafke matar ne bayan samun labari cin zarafin almajirin ta hanyar neman sa da ya riƙa biya mata buƙata irin ta mata da miji. Ya ce almajirin da kansa ya gudu ya nemi mai unguwa domin a kuɓutar da shi daga wannan hali da ta sanya shi ciki.

Don haka suka kai rahoton ga Hukumar Tsaron Farin Kaya Sibli Difens (NSCDC) aka kamo ta aka yi mata binciken kwakwaf, daga nan aka kai ta Bauchi ofishin masu binciken manyan laifika (CID) don kammala binciken kafin a mika ta ga kotu.

Wata majiya ta ce wajen da matar take sana’ar dan waken ya zama babban dandalin ɓarayi da ’yan shaye-shaye da ƙananan mata masu zaman kansu, domin duk wadda aka kama a samame, takan ce a wajen baba mai ɗan wake take.

Da aka tambayi almajirin abin da ke faruwa tsakaninsa da ita? Ya ce da farko bara yake zuwa, sai ta ce, ya rika zuwa gidanta tana ba shi abinci.

Ya ce da yake zuwa gidanta bayan ta tashi a kasuwancinta, sai ta riƙa kai shi ɗakinta tana ba shi abinci da lemon kwalbar da take sa maganin a ciki, tare da umartar sa ya riƙa matsa mata jikinta daga nan sai ta rika jan sa kanta tana kama gabansa tana sawa a cikin nata.

Yaron ya ce haka suka rika yi tun kafin azumi har bayan azumi, alhali shi ba abin da yake ji sai ciwon baya da yake addabar sa, wanda hakan ta sa ya gudu ya yi ƙara wajen mai unguwa.

Yanzu dai Shugaban Ƙungiyar Alarammomi na Ƙasar Katagum, Alaramma Husaini Gwani Gambo da Ƙungiyar Mata Musulmi ta FOMWAN da Ƙungiyar Matasa Masu Neman Hakkin Dan Adam, sun sa hannu don ganin an yi hukunci a kanta da bukatar tashinta a garin Azare.

Shugaban ƙungiyar alarammomin ya tabbatar da cewar, za su yi duk yadda za su yi don ganin an bi musu hakkin wannan cin zarafin da aka yiwa almajirinsu ba don ganin ya zama darasi ga wasu irin ta.