Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta rufe wani shagon da ake yin caca na zamani, wanda aka fi sani da “betting”.
Mataimakin kwamandan hukumar a Kano, Sheikh Mujahideen Aminudeen, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Kano.
- Kotu ta yanke wa dillalan ƙwayoyi hukuncin ɗaurin shekaru 95
- Kisan malami: Shugabannin Kiristocin Kudancin Kaduna sun yi Allah-wadai
Ya ce sun ɗauki wannan mataki ne bisa dokokin Jihar Kano, kuma hukumar ta kai samame wajen kafin ta rufe shagon gaba ɗaya.
Aminudeen ya nuna damuwa kan yadda wasu Musulmai ke shiga harkar caca, musamman a lokacin azumin watan Ramadan.
A watannin baya hukumar ta haramta yin cacar “betting” lamarin da ya sanya ta fara farautar wuraren da ake yin cacar domin rufe su.
An fara aiki da dokokin shari’ar Musulunci a Kano tun shekarar 2000, kamar yadda ake yi a wasu jihohi 11 na Arewacin Najeriya.
Waɗannan dokoki sun haramta caca, karuwanci da shan giya a jihar.