Wani magidanci ya danƙara wa matarsa saki a ofishin ’yan sanda bayan an kama ta a wani otel.
Wani jami’in tsaro ya bayyana cewa an kama matar ce a yayin wani samame da ’yan sanda suka kai maɓoyar dillalan miyagun ƙwaya da ’yan sara-suka a wasu otel-otel a garin Minna.
Ya bayyana cewa sai bayan da aka kawo matar ofishin ’yan sanda, a yayin bincike suka gano cewa matar aure ce, bayan da suka tuntuɓi ’yan uwan mutanen da aka kama.
Ya ce, “Sakamakon yawaitar yadda matasa suke tayar da zaune tsaye ne mataimakin gwamna Kwamred Yakubu Garba, ya umarci jami’an tsaro su ɗauki mataki a kansu.
- Yadda uba da ɗansa da wani ango suka rasu a bakin aiki a Bauchi
- Fafaroma Frasncis ya rasu yana da shekaru 88
“Shi ne muka kai samame, muka kama mutanen da ake zargi, cikinsu har da mata. Abin mamaki sai ga wani mutum ya zo, cewa ɗaya daga cikin matan da muka kama mai ɗakinsa ce, kuma nan take ya yi mata saki uku.
“Ba mu san cewa matar aure ba ce, kuma ba mu da masaniyar abin da ya kai ta wurin, domin ’yan sanda ba su kammala bincike ba lokacin da mutumin ya je ya ba ta takarda a ofishin ’yan sanda.”