Da safiyar wannan Litin fadar Vatican ta sanar cewa da misalin ƙarfe 7.35 Agogon Vatican Fafaroma Francis, wanda sunansa na asali Cardinal Jorge Mario Bergoglio, ya rasu a yayin da al’ummar Kirista na duniya ke bikin Ista.
Ya mutu ne washegari da ya fito bainar jama’a a Dandalin St Peter’s, domin taya Kiristoci murnar zagayowar ranar Ista.
Fafaroma Francis ya yi fama da doguwar jinya, inda a watan da ya gabata ne aka sallame daga asibiti bayan ya shafe makonni biyar can sakamakon cutar sanyin haƙarƙari mai tsanani.
Ga wasu abubuwa da Fafaroman ya yi fice a kansu:
1. Nuna adawa a fili ga wasu daga cikin manufofin Donald Trump.
Ya yi Allah wadai da yunƙurin Trump a mulkin sa na farko na gina katanga tsakanin Amurka da Mexico, inda yace hakan ba ɗabi’ar kiristoci bace.
Ya kuma yi Allah wadai da shirin maida baƙi ƙasashen su, da gwamnatin Trump ke ƙoƙarin yi a mulkin sa na biyu.
2. Sunbatar ƙafafuwan fursunoni.
Fafaroma Francis ya wanke tafin ƙafafuwan wasu fursunonin gidan yarin Rome, tare da sunbata, abun da yaja hankalin duniya.
3. Kira a magance matsalar sauyin yanayi.
Fafaroma Francis ya zargi manyan ƙasashen duniya da ƙin ɗaukar matakan kare muhalli da sauyin yanayi, inda a 2023 ya ce wasu matsalolin ba za su taɓa gyaruwa ba.
4. Jawo masu ɗabi’ar auren jinsi a jiki.
Duk da kakkausan suka da ya sha, wasu na ganin yana da ƙoƙarin jawo masu raunin imani a jiki, ciki kuwa har da yarda da yayi ake sanya albarka ga auren jinsi.
5. Shi ne Fafaroma na 266, kuma na farko daga nahiyar Arewa da kudancin Amurka.
Asalin iyayen sa ƴan Italiya ne, da suka yi ƙaura zuwa Argentina. An haife shi a Buenos Aires, ranar 17 ga watan Disamba, 1936.
6. Ya yi kakkausar suka ga kamfanonin ƙera makamai.
Ya yi kira ga ƙasashen duniya da su rungumi masalaha wajen magance rigingimu, gudun kada rikice-rikice su haifar da yaƙin duniya na 3.
7. Ya alaƙanta kwararar ƴan ci rani zuwa Turai, da tauye ci gaban ƙananan ƙasashe.
Ziyararsa ta farko, Francis ya je tsibirin Lampedusa, yankin da ƴan ci rani suke bi wajen shiga nahiyar Turai, inda ya ɗora laifi kan yadda ake tauye ci gaban ƙananan ƙasashen duniya.
8. Yana son nishadi irin na ƙwallon ƙafa da kuma waƙe-waƙe.
Fafaroma Francis shine Paparoma da yafi mu’amala da matasa, wajen sauraron su, da kuma ƙaunarsa da ƙwallon ƙafa.