A safiyar jiya Litinin ce Fafaroma Francis mai shekaru 88 ya koma ga mahaliccinsa, bayan da ya yi fama da mutuwar ɓarin jiki da kuma bugun zuciya, kamar yadda Fadar Vatican ta sanar.
Shugaban na mabiya ɗariƙar Katolika ya shafe makonni 5 a asibiti a farkon wannan shekara, sakamakon harbuwa da cutar limoniya, amma ya koma gida a watan da ya wuce, bayan da ya samun sauƙi.
Fadar Vatican ta tabbatar da cewar a ranar Asabar ne za a gudanar da jana’izar Fafaroma Francis a majami’ar St. Peter’s Basilica.
A safiyar Talatar nan ce dai fadar Vatican ta saki hoton Fafaroma Francis kwance a cikin akwati a majami’ar Santa Marta, inda ya zauna tsawon shekaru 12 a matsayin Fafaroma.
Manya-manyan limamin cocin Katolika a Fadar Vatican da ake kira Cardinals za su yi wani taro domin shirya jana’izar Fafaroma Francis, gabanin zaɓen sabon Fafaroma a wata mai zuwa.
Gwamnatin Italiya ta ayyana makokin kwanaki biyar
Gwamnatin Italiya ta sanar da zaman makoki na kwanaki biyar domin alhinin rasuwar shugaban darikar Katolika na duniya fafaroma Francis, fiye da makokin kwanaki uku da aka yi lokacin rasuwar Fafaroma John Paul na biyu a shekarar 2005.
Za a ci gaba da zaman makokin zuwa ranar Asabar, ranar da za a yi jana’izar marigayi shugaban na Katolika.
Za a yi jana’izarsa a dandalin St Peters Basilica kamar yadda ministan tsaron al’umma Nello Musumecci ya shaida wa ’yan jarida bayan taron majalisar zartarwar gwamnati. An sassauto da tutar ƙasar a gine ginen gwamnati.
A halin da ake ciki an tsaurara matakan tsaro a Rome, babban birnin kasar Italiya gabanin ranar jana’izar.
Shugabannin duniya za su halarci jana’izar
Ana sa ran manyan jami’ai daga sassa da dama na duniya za su halarci jana’izar.
Tuni dai wasu daga cikin manyan shugabannin ƙasashe suka bayyana aniyarsu ta halartar jana’izar Fafaroma Francis, cikin su kuwa har da Donald Trump na Amurka da Emmanuel Macron na Faransa.
Sauran sun haɗa da shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky da Firaministan Australia Anthony Albanese.
To sai dai Fadar Kremlin, ta ce shugaba Vladimir Putin ba zai samu damar halartar bikin jana’izar ba.
Shin Fafaroma na gaba zai fito daga Afirka?
A lokacin da ake jimamin rasuwar shugaban darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis, ana ci gaba da dakon sunan magajin Fafaroman da ake hasashen ka iya fito wa daga nahiyar Afirka.
Wata majiya daga fadar Vatican ta ce mutane aƙalla 15 daga nahiyoyi daban-daban suka cancanci maye gurbin shugaban darikar katolika na duniya, wanda ya rasu a ranar 21 ga watan Afrilu.
To amma komai zai iya faruwa a zaben jagoran fadar ta Vatican domin kuwa dan Afirka ka iya kasancewa lamba daya a jagorancin darikar Katolika na duniya.
’Yan Afirka biyu zuwa uku ne dai ke sahun gaba a wajen maye gurbin Fafaroma Francis, duk da cewa tasirin mulkin mallaka da wariyar launin fata da wasu dokoki da ka’idojin ka iya kasancewa tazgaro wajen burin Afirka na samun wannan kujera mafi girma a duniya.
Kwararren jami’in diflomasiyyar nan ɗan asalin Ghana, Cardinal Peter Affiah Turkson mai shekara 76, na cikin waɗanda ake hasashen zai iya zama Fafaroma.
Turkson ya san sirrin fadar kuma yana daya daga cikin wadanda suke bai wa Fafaroma Francis shawara kan siyasa da diflomasiyyar duniya, kuma ya taka rawa wajen tabbatar da wanzar da zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu.
Mutanen Ghana na cike da burin samun lamba ɗaya a darikar ta Katolika, kamar yadda a baya ɗan asalin ƙasar, Mista Kofi Annan ya zama shugaban Majalisar Dinkin Duniya daga Ghana.
Cardinal Fridolin Ambongo Besungu mai shekara 65, daga Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na daga cikin farin wata sha kallo a matsayin magajin Francis.
Shi dai Besungu na gaba-gaba wajen gangamin tabbatar da adalci da daidaito a tsakanin al’umma, kuma ya yi kaurin suna a lokacin da ya sanya albarka kan masu muradin auren jinsi daya, wanda hakan ya haifar da cece-kuce a duniya.
A baya ma dai an samu ɗan Tarayyar Nijeriya da ya kai matsayin zama shugaban darikar Katolika na duniya wato Cardinal Francis Arinze, to amma shekaru sun cimma Arinze kasancewar ya haura shekaru 90.
Jorge Mario Bergoglio, shi ne jagoran Katolika na farko da ya fito daga Latin Amurka, kuma kasashen duniya na ci gaba da nuna alhinin rasuwarsa, tare da aike sakonnin ta’aziyyarsu.
Limamai 135 za su zaɓi sabon Fafaroma
Haka kuma, wasu manya-manyan limamin guda 135 ne da ake kira Cardinals za su yi zaɓen sabon Fafaroma a wata mai zuwa yayin da aka ayyana gurbin marigayi Fafaroma Francis a matsayin “sede vacante” alamar cewa babu mai jagoranci a kan kujerar Fafaroma.
Duk da cewa a halin yanzu akwai manyan limamai 252, amma 135 ne kacal za su iya zaɓen sabon Fafaroma saboda rahowar sun haura shekaru 80 a duniya, wanda sharadi ne na duk wanda ya haura shekarun ba zai yi zaɓe ba, sai dai suna iya bayar da shawarwari da kuma shiga muhawarar zaɓen sabon Fafaroma
TDaga cikin wadanda ake hasashen za a zaɓi Fafaroma na 266 kamar yadda BBC ya rairayo akwai:
Cardinal Luis Antonio Tagle (Philippines)
Cardinal Pietro Parolin (Italy)
Cardinal Péter Erdő (Hungary)
Cardinal Raymond Leo Burke (USA)
Cardinal Matteo Zuppi (Italy)
Cardinal Willem Jacobus Eijk (Netherlands)
Cardinal Mario Grech (Malta)
Cardinal Peter Turkson (Ghana)
Cardinal Angelo Scola (Italy)
Cardinal Pierbattista Pizzaballa (Italy)
Kar a binne ni a kabari mai ado — Fafaroma Francis
Fafaroma Francis ya bayyana abin da yake so a yi bayan mutuwarsa a wasiyyarsa, inda ya nemi a binne shi a wani kabari mara ado, a cocin da yake so a Roma, Santa Maria Maggiore.
“Yayin da nake jin cewa rayuwata a duniya ta kusa zo ƙarshe kuma tare da karsashin fatan Rayuwa Madawwamiya, ina son in bayyana wasiyyata game da inda za a binne ni ne kawai,” kamar yadda Fafaroma ya bayyana a wasiyyarsa da ya rubuta ranar 29 ga watan Yuni, ta shekarar, 2022, da fadar Vatikan ta wallafa ranar Litinin.
“Ina neman a binne gawata domin ta jira tashin ƙiyama a cocin Fafaroma na Santa Maria Maggiore,” in ji Fafaroman, wanda ya yi ta neman ziyartar muhimmin wurin mai tsarki na Katolikan kafin da kuma bayan ko wace tafiyar da ya yi a matsayinsa na Fafaroma.
A wasiyyarsa, Francis ya bayyana daidai wurin da yake so a binne shi tare da bada wani zane domin bayyana yadda yake so a binne shi, kuma ya ce an riga an ƙayyade kuɗin da za a kashe wajen binne shi.
“Dole kabarin ya kasance a doron ƙasa na duniyar Earth, gaya, ba tare da wani ado ba kuma ya kasance da rubutun da ke cewa: Franciscus.”
A ƙarshen wasiyyarsa, jagoran addinin ‘yan Ɗrikar Katolika na Duniya ya nemi Allah ya “ya bada ladan da ya kamaci waɗanda suke so na kuma za su ci gaba da yi mini addu’a “.
“Na ba da wahalar da na sha a ƙarshen rayuwata ga Allah domin zaman lafiyar duniya da kuma ‘yanuwantaka tsakanin mutane.”