An sace wani Kuros da tsohon Fafaroma, Benedict XVI ya bayar da kyautarsa ga wani coci da ke garinsa na Bavaria a kasar Jamus.
A cewar ’yan sanda, an sace kuros din ne wanda ke makale a jikin bangon cocin, wanda aka ajiye a matsayin kayan tarihi.
- Dillalan naman jaki na neman diyyar biliyan daya daga hukumar Kwastam
- Tsananin zafi ya yi ajalin kusan mutum 100 a India
Sashen binciken manyan laifuffuka na ’yan sandan kasar ya ce wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba suka fasa cocin sannan suka sace kuros din a ranar Litinin.
Ana ganin kuros din a matsayin wata alama ta tarihi. ’Yan sanda sun kuma ce an sace makuden kudade a cikin cocin, kamar yadda kafar yada labarai ta ABC ta rawaito.
“Wannan kuros din na da matukar muhimmanci ga mabiya darikar Katolika,” kamar yadda sanarwar ’yan sandan ta ce, tana mai kira ga wadanda suka ga mutanen da ake zargi da satar da su gaggauta sanar da su.
Marigayi Fafaroma Benedict dai ya rasu ne ranar 31 ga watan Disambar 2022, bayan kusan shekara 10 da kafa tarihin zama Fararoma na farko da ya ajiye mukaminsa cikin kusan shekara 60.
Limamin cocin birnin Munich, Christoph Kappes, ya ce irin kuros din da aka sace ba shi da yawa a duniya.