A jawabin da ya saba yi albarkacin bikin Kirsimeti, Fafaroma Francis, ya bukaci a gaggauta kawo karshen abin da ya kira da “rashin hankalin” yakin Ukraine.
Shugaban na darikar Katolika ya yi jawabin ne a gaban dubban Kiristocin da suka taru a dandalin St Peter’s da ke birnin Roma ranar Lahadi, wasun su rike da tutar kasar ta Ukraine.
Galibi dama jawabin na Fafaroma da ake yadawa kai tsaye duk ranar Kirsimeti, don murnar zagayowar ranar haihuwar Yesu Almasihu, kan mayar da hankali ne wajen kira ga samun zaman lafiya
A cewarsa, “’Yan uwanmu ’yan kasar Ukraine na bikin Kirsimetin na bana a cikin duhu da sanyi, kuma a nesa da gidajensu.
“Muna addu’ar Allah Ya ba mu damar taimaka musu kan matsananciyar bukatar da suke ciki, kuma muna da Muryar da ya kamata mu yi kira da ita a kawo karshen wannan rashin hankalin ba tare da bata lokaci ba,” inji shi.
Fafaroma Francis ya kuma ce abin takaici ne yadda duniya ta ki ta koma ga Allah wajen samun mafita ga matsalar yakin da ake ciki.
Ya kuma ce duniya a yanzu na fuskantar yanayin yakin da ya ce kusan shi ne Yakin Duniya na Uku.
Ya kuma ce akwai kasashe da dama da ke bikin Kirsimetin cikin kunci, ko dai ta sanadin yaki ko kuma sauran matsaloli kamar a kasashen Afghanistan da Yemen da Siriya da Myanmar da Lebanon da Haiti da kuma rikicin Isra’ila da Falasdinawa.
Sai dai a karon farko, Fafaroman ya bukaci a tsagaita wuta sannan a samo mafita ta hanyar tattaunawa kan zanga-zangar da mata ke gudanarwa a kasar Iran tsawon wata uku ke nan.
A baya dai, Fafaroma ya sha kiran da a sami zaman lafiya a rikicin Rasha da Ukraine, tun da aka fara shi a watan Fabrairun bara, kodayake ana ganin kamar ya fi zama a tsaka-tsaki.
Sai dai an sha sukar lamirinsa kan cewa ya ki kausasa kalamai kan Shugaban Rasha Vladimir Putin saboda mamaye Ukraine din.