Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, tare da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa, har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, muna nan dai a kan hanyarmu ta zuwa Aljanna. Mun kwana bayan mun jero wasu sinadarai da za su taimaka mana a cikin wannan tafiya, wadanda suka hada yin da’a ga iyaye da kyautata musu; sadar da zumuntarmu; kyautata wa makwabta da bako; girmama Musulmi da ba shi hakkokinsa, yadda ya kamata; da kuma yin adalci a cikin al’amurranmu na rayuwa ta kowane gefe, wanda yin haka zai sa al’amarin kasa da na al’ummar cikinta ya tsayu, ya gudana yadda ya kamata! Arziki ya yalwata, zaman lafiya ya samu!
Yau kuma ga ci gaba:
Shaihin Malami, Abubakar Aljaza’iriy ya ce, to yanzu fa mun kawo rabin tafiyarmu, ba abin da ya rage sai sauran rabin kusan karshe, wanda shi ne barin shirka da sabo. Saboda haka, kada mu tsaya, ku zo mu ci gaba da tafiya, ba tare da wata sarewa ko nuna gajiya ba.
Lallai ne mu yi nesa da shirka (hada wani da Allah cikin bauta), wato:
1. Kada mu kudurta cewa wani daga cikin halittu, kowane ne shi daga cikin halittun, kowane irin matsayi yake da shi, yana iya mallaka wa kansa ko waninsa wata cutarwa ko wani amfani, in ba tare da son Allah ba da kuma ikon Allah. Babu wani da zai iya mallakar wani abu wurin Allah, sai in Allah din Ya so. Saboda haka lallai mu takaita kwadayinmu na duk abin da muke so kuma muke nema, ya kasance a wurin Allah ne kadai, muke so ko muke neman abin. Mu saki kowa, mu kyale kowa, don wannan da muke nema wurinsa, in dai ba Allah ba ne, to bai iya kawo amfani, balle ya iya kawo cuta! karshenta ma wajen neman amfani, sannan ne za a cutu. Kada mu yi kwadayin komai wajen wani, in ba wurin Allah ba! Kada mu nemi komai wajen wani abin halitta, na daga ceto ko agaji, wanda ba mai bayar da kowanensu, in ba Allah kadai ba. Don haka mu takaita (mu tsayar da) kwadayinmu da tsoronmu (na abin da ke tsorata mu ko yake tayar mana da hankali, mu nemi kariya daga Allah) da bukatarmu, duk mu mayar da su ga Allah kadai!!
2. Kada mu kuskura mu yi wani aiki na ibada (bautar Allah) don wanin Allah. A’a, duk abin da za mu yi, to, ya kasance mun yi shi don Allah kadai – ikhlasi – Kada mu yi rantsuwa, misali, ba da Allah ba, wato kada mu zo rantsuwa mu ce “aradu” ko “tannatsa” ko “gajimari” ko “rawanin shehu” ko “kabarin tsoho” ko “waliyyi wane,” – duk wadannan haram ne. Yin irin wannan rantsuwa, saba wa ka’ida ne; in za a rantse, to a rantse da Allah – duk wanda zai yi rantsuwa to ya rantse da Allah ko ya yi shiru! –kamar yadda ya zo a Hadisi.
Kada mu je mu yi yanka a kabarin wani waliyyi daga waliyyan Allah. A’a, mu kyale su, don su ma Allah ne Ya shiryar da su yadda za su bauta wa Allah, suka yi kamar yadda ya dace da bin sunnar Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), suka kai ga wannan matsayi. Saboda haka mu ma sai mu yi ta kokarin yin yadda suka yi, har suka samu wannan matsayi, kada mu dauki wani hakkin da ba nasu ba mu ba su. Wasu ma ba su ba ne, karya aka yi musu, daga baya aka komo ana yi musu abin da ba su ce ba.
Kada mu yi wani alwashi ba na Allah ba. Kada mu kira wani, wanda ba Allah ba. Kada mu nemi agajin wani, wanda ba Allah ba.
3. Kada mu kuskura mu rataya wani zare ko kashi ko karfe, wai mu ce yana tunkude wata cuta, kamar yana maganin mayu ko wani abin da ya yi kama da haka. Da yawa za ka ga wani ya kafa wani abu a kofar gida ko dakinsa, kamar kahon ragon layya, wanda in aka tambaya, mutum yana cewa, wai “kafi ne!” To, yaya aka yi shi ragon ya bari har aka yanka shi? Ko wani ya kawo kaho ko wani yanki na jikin gada ko barewa, ya sanya. To, ita ma in tana da wannan magani, yaya aka yi har aka kamo ta a daji, ba ta kafe ba, ta sha (ta tsere)? Ba ta kare kanta ba a lokacin tana da rai, sai bayan ta mutu, sai a ciro kahonta a sa a gida, a ce zai yi wani tasiri? karya ce wannan! Saboda haka, kawai mutum ya dogara ga Allah! Ka karanta azkar (zikirori) na neman kariya, kamar yadda shari’a ta aje! In ka yi haka, kuma wani abu ya same ka to, ka gane cewa wannan wani sababi ne da yana yiwuwa za a daukaka ka ne zuwa wani matsayi na rayuwa da shi.
Lallai mu kudurce cewa ba mai maganin wani matsatsi ko tunkude wata cuta, sai Allah, Tabaraka Wa Ta’ala, kadai!
4. Kada mu yarda mu gaskanta boka ko mai duba ko (mai aiki da) taurari ya buga kasa, ya ce ai ya duba ya gano cewa za ka samu kaza. To, me ya sa bai dubo wa kansa, aka ba shi abin ba, sai kai da ya maida wawa ko dolo?
Bokaye suna yaudarar mutane fiye da misali. Wasu har lokacin da za su tafi aikin Hajji, sai sun yi shirka! Su debo kashin abu kaza, ku yi abu kaza, wanda ko kusa bai dace da shari’a ba. Wasu ka gan su a Arafa suna tsince-tsince. Wasu a wajen Safa da Marwa! Kai, abin dai ba iyaka. Duk bokaye ke sanya su yin haka. Akwai wadda ma ta yi kashi a Ka’aba, ana cikin dawafi sai ta yi zawo, kuma da gangan, domin lokacin da aka tambaye ta, yaya aka yi sai ta ce, an ce in ta yi zawon, za ta kasance ba wanda ya fi ta kudi a garinsu.
Yau abin ya kai ma har ana fada wa mutum makomarsa a rayuwa, in aka duba tafin hannunsa! Har matasa, abin bakin ciki, ba a bar su a baya ba. Sai a fada wa mutum wai ga abin da zai samu ko ga abin da zai zama. Ko a ce a sa rana da shekarar haihuwa, wai za a fada wa mutum makomarsa. Duk karya ne! Ba mai ilimin wannan, sai Allah Tabaraka Wa Ta’ala!
Mu kwana nan!