✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsokaci game da hanyar zuwa Aljanna (4)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga mafificin…

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, tare da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa, har zuwa Ranar Sakamako.

Bayan haka, yau ma ga ci gaban tsokacinmu na hanyar zuwa Aljanna:
Manufa ita ce, farkon abin da ake bukata shi ne kudurcewa da tabbatarwa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Mai gafara, Mai sa soyayya, Wanda Yana son bayinSa, Yana sa soyayya tsakanin bayinSa. Saboda haka a bauta maSa, Shi kadai da imani da gamsuwa ta yakini (sakankancewa da yarda), sannan da yi maSa da’a, kan cikakkiyar gaskiya da ikhlasi – tsarkake aiki gare Shi, Shi kadai (kada a hada kowa da Shi cikin bautar). Sannan kuma a bi ManzonSa, (SAW) shi ma da gaskiya (a gaskanta shi) a cikin duk abin da ya ba da labari. A yi biyayya gare shi, gwargwadon iyawa, kan abin da ya umarta, kuma a nisanci duk abin da ya hana, ya yi kwabo a kansa. A lura cewa shi Annabi Muhammad, (Sallallahu Alaihi Wasallam), shi ne Manzo, kebantacce a kan bayanin yadda za a bauta wa Allah, Shi kadai a nan duniya. Shi kadai ne (Manzon Allah, Sallallahu Alaihi Wasallam) zai bayyana yadda za a yi wannan bautar. Duk wani wanda zai yi bayani, sai dai ya kwaikwayi nasa, kan yadda sahabbai suka bayyana, amma ba ya kawo nasa ba.
Ba ya yiwuwa ga wani ya bauta wa Allah ba tare da shiryarwar Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam) ba, tare da bayanin yadda za a yi bautar. Saboda haka duk wanda ya ki yarda da bayanin da Annabi (SAW) ya yi a kan ibada, ko na wa ya bi, ba zai tsira ba a Lahira! Lallai ya sani, in ya ki bin Manzon Allah (SAW) game da yadda za a yi wannan bauta, ya yi aikin banza, ya yi asara!
Shi ke nan, yanzu ya ’yan uwana, sai mu kama hanyar nan, tunda dai kun ji bayani kuma kowa ya yarda, ya gamsu da al’amarin kalmomin “La’ilaha illallah Muhammadur rasulullah!” Shi ya sa wanda bai fade ta (kalmar akidar nan) ya yarda da ita ba, ba a kai shi masallaci, ba a ba shi Alkur’ani don ya gudanar da wani abu na ibada. Ba ya yin komai na Musulunci, a ce ai ya yi addini, sai in ya fade ta, ya yarda da ma’anarta, bayan an fassara masa kuma ya gamsu da hakan, sannan yake zama Musulmi, wanda za a tafi da shi a kan wannan hanyar.
Tunda mun kama hanya, lallai ne:
1. Mu kasance masu kudurcewa ba mu da wata tantama a zukatanmu, muna masu jajircewa cewa Mahaliccinmu, Tabarka wa Ta’ala, Shi ne Wanda Ya halitta duniyar nan gaba daya. Ya tsara sama da kasa da ikonSa da saninSa da sonSa (ganin damarSa – duk yadda Ya so abinSa haka yake kasancewa), sannan da hikimarSa (Tauhidin Rububiyya ke nan!) Da wannan ne kuma aka gano Yana da sifofi madaukaka da sunaye kyawawa (wadanda suka fi kyau). Da ikonSa ne, wadannan halittu suka kasance, ba a taba samun wani tazgaro a cikinsu ba. kasa tana juyawa, ba mu ma san tana juyawa ba, kuma da ilimin Allah ne ya zama wannan saman ta samu, al’amarinta ya zama jere, ana ganinta a tsare, ta kai matsayin da take din nan, a kan wani tsari mai ban sha’awa, mai burgewa. Kai da kallonta, ka yaba, ka ce, “Lallai mai saman nan ya iya aiki, kuma yana da kayan aikin.” Ku kwatanta ku gani, misali idan wani zai yi gini mai hawa daya, ku ga irin hakilon da za a yi da irin dogon lokacin da za a dauka kafin a ce an gama, an kai ga cin nasara a kan ginin.
2. Mu kudurce, muna masu yankewa ba mu yin shakka, cewa babu wani da zai iya yin hadaka da Allah cikin abubuwan halittar nan naSa; ba wani wanda yake ji a jikinsa cewa da nasa a ciki, kuma babu mai taya Shi gudanarwa, Shi ke gudanar da abinSa, Shi kadai da kanSa. In da akwai wani a cikin wannan gudanarwa, lallai da an samu matsala – domin za a samu karo da juna, za a samu tufka da warwara. Tunda wannan zai ce a yi kaza, wancan ya ce ba za a yi ba! Ko wannan ya ce a bari, wancan ya ce sai an yi! Haka nan, in da akwai wannan, lallai da yanzu saman nan (kai halittar gaba daya) ta kare! Da sai a wayigari wata rana ba ta nan! Allah Ya ce, “Ka ce, (ya Muhammad!) Da a ce akwai wani abin bauta tare da Allah, lallai da saman nan ta rushe! Don haka tsarki ya tabbata ga Allah, Ubangijin Al’arshi daga abin da suke siffanta Shi da su.”
3. Mu kudurce, tunda dai Allah ba Shi da abokin hadaka cikin halittar nan da gudanar da ita, to, lallai ne mu hakkake cewa Mai aikin nan, Shi kadai ne Ya cancanta a bauta maSa. Saboda haka sai a yanke a nuna cewa lallai Mai wannan Shi kadai Ya cancanci a yi maSa da’a. Bai dace ba, kuma ba ya halatta a hada wani tare da Shi a bauta maSa har abada. Kowane ne shi – Mala’ika ne makusanci; ko Annabi ne da aka aiko; ko wanda ba su ba daga cikin sauran halittu. – Kuma babu bambanci, ita ibadar nan Sallah ce ko addu’a ko azumi ne ko yanka ko zakka ko alwashi ko neman agaji ko wani abin da ya yi kama da haka, wanda Shi kadai ne ke iya yi, ba za a yi wa kowa daya da cikin wadannan ba, sai Allah kadai! Ko kuwa wata biyayya (ga wani) a wajen saba wa Allah Ta’ala ta fuskar haramta abin da Ya halatta, ko halatta abin da Ya haramta. Ko kuma a kyale abin da Allah Ya wajabta ko kuma a aikata abin da Ya haramta, saboda wani. Ko wa ya ce a yi haka, ba za a bi shi ba! In an yi haka, wato an bi tsarin da aka ajiye, an tabbatar da gaskiya ke nan.
4. Mu kudurce, muna masu tabbatarwa cewa bukatar da al’umma take da ita ga Annabawa da Manzanni (Masu Amincin Allah – wadanda Manzon Allah shi ne na karshensu), wadanda za su nuna musu hanyar zuwa Aljanna, shi ne dalilin aiko su. Dalilin da ya sa aka aiko Annabawa, shi ne don su nuna wa al’umma hanyar da za a bi don komawa cikin wancan gida da Shaidan ya fito da babanmu (Annabi Adam AS) daga cikinsa. Wannan ita ce hikimar aiko Manzanni.
Mu kwanan nan!