Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, tare da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa, har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, yau kuma mukalar tamu za ta ci gaba ne daga inda ake son:
A gane cewa ita shari’ar nan ka’ida ce, wadda an gina ta a kan abubuwa biyu kacal: (1) Yi don Allah kadai (ikhlasi) da (2) Kwaikwayon Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam).
Saboda haka, in an je Lahira, ayyukan mutum gaba daya, za a tara su ne a sa musu alamomin tambaya cewa, “Me ya sa ka yi aikin?” da kuma, “Wa ya koya maka aikin?” Wallahi, in ba daya a cikin biyun nan (wato yi don Allah; da kuma kwaikwayon Manzon Allah SAW), ba za a tsira ba. Shi ya sa ( Manzon Allah, Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce, a wancan Hadisi na biyu, “…duk wanda ya saba min to, ya ki, ya juya baya, ba ya son shiga Aljanna…”
Malam Aljaza’iriy ya ce, “Saboda haka shi (Annabi), wanda Tsira da Amincin Allah suka tabbata a gare shi, a cikin wadancan Hadisai biyu da suka gabata, ya bayyana hanyar nan (ta zuwa Aljanna), ya zayyana ta a fili ga duk wanda yake da basira (hankali da tunani). Don haka, sai ku zo mu je kan hanyar nan ya ’yan uwana, mu tafi tare muna ’yan uwan juna, muna nuna soyayya ga juna, kuma abokan juna, masu taimakekeniya ga juna. Ta yadda in ma muka ga wani zai gaza, ya sare, kamar ya gaji da tafiya, mu kama hannunsa mu jawo shi.”
Idan ana tafiya kan tsari na Musulunci, sai ka ga wani yana yin baya-baya, to a matsa can gaba, a jira shi, a jawo shi. Rago da haka yake kaiwa garin da za a je, in dai ana jiransa, wani sai ya kawo! Amma in aka yi ta tafiya, ba a jiransa, sai ya sare a hanyar, ko kuma ya koma baya. Don haka, mu kasance masu taimakekeniya a cikin wannan addini a tsakanin junanmu.
Ko sahabban Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam, ba karfin imaninsu daya ba. Wasu suka rika jan hannun wasu, har aka kai inda aka kai, (Allah Ya kara musu yarda).
Yanzu, a misali, idan mutum yana da birbishin imani, sai aka yi mako guda ba a gan shi a Sallar Asuba ba, sai ya ga an je gidansa an ce, “Wane zuwa muka yi mu duba, don mun ga kwana biyu ko lafiya, ana ta Sallar Asuba ba ka zuwa?” Ai wani daga nan zai ji kunya ya ce, “Kai, ai wallahi, kwanan nan nauyin bacrci yana damuna.” Sai su ce, “To, ba komai, gobe in ba mu ganka ba, za mu bugo maka waya don tayar da kai.” Saboda haka dai taimakon juna ake so a rika yi a cikin wannan al’amari, har a kai ga tsira tare. Allah Ya ba mu dacewa!
Yanzu ga shi mun hau hanya:
Malam Jaza’iriy ya ce to, ku biyo ni don in yi muku jagora, don in nuna muku ita wannan hanya har zuwa Aljannar Ubangiji, wadda gida ne da in kun shiga ba za ku fita ba, kuma kuna wadanda ake karramawa, masu daraja, cikin jin dadi da nishadi.
Sai dai ku lura, ita hanyar nan, ya ku ma’abuta wannan tafiya, tana nan tsakanin kalmomi hudu, wadanda za mu rike, mu kankame kuma mu lura da su, domin su ne kayan tafiyar, su ne guzuri. Biyu, wadanda ake korewa ne, ba a son mu aikata su. Sauran biyun kuma, so ake mu yi su, mu rike su kamkam, kada mu rabu da su, har mutuwa.
Wadanda ba a so din nan da ake son mu kore su, mu raba kanmu da su, su ne ‘Shirka da Sabon Allah.’ Mu yi kokari, duk yadda za mu yi, kada mu kuskura mu hada wani da Allah wajen gudanar da ayyukanmu na bauta maSa. Kuma mu yi duk yadda za mu yi, mu daina sabo, ta yadda da mun gano mun yi ba daidai ba za mu tuba, mu koma iyakar kokarinmu mu gyara! Ta yadda muna cikin tafiyar, akan zame; da mun zamen nan, sai mu yi sauri mu tuba, mu koma hanya. Haka dai, haka dai, har zuwa ranar mutuwa, kuma in aka yi sa’a ka tuba da safe, ka wanke komai, kafin rana ta yi Allah Ya karbi kayanSa. Shi ke nan, cikin yardar Allah, an samu husunul khatimah (cikawa kyakkyawa). Allah Ya ba mu kyakkyawar cikawa, in karshenmu ya zo!
Su kuma wadanda ake son mu rike mu kankame su, mu yi ta yi har iyakar rayuwarmu su ne ‘Imani da Ayyukan kwarai!’
Daga wadannan kalmomi guda hudu ake tattara guzurin yadda za a bi wannan hanyar, wadda, kamar yadda bayani ya gabata, hanya ce kai-tsaye, mikakkiya da ba za ta zarce ko’ina ba, sai gidan can na Aljannah, gidan zama, gidan karamci da natsuwa da kwanciyar hankali har abada!
Farkon hanyar ke nan – Akidah – wato ambato da kudurce ‘La’ilaha illallah Muhammadur Rasulullah!’ (Wato babu abin bauta wa bisa cancanta sai Allah, Annabi Muhammadu Manzon Allah ne). Wannan bangare na akidar nan, in babu shi, to duk ayyuka babu su, ko an yi su, to duk sun lalace. Shirka, idan an yi ta, to komai na aikin ibada ya lalace. Misali yanzu idan aka ce ga wagegiyar tunkuyar fate a gidan biki, sai yaro ya zo da dan karamin abin kashinsa (fo), ya tsoma a cikin tukunyar nan – ana ganin, saboda dan karami ne, za a ci gaba da cin faten nan, kuma faten yana nan lafiya lau? To, haka shirka take da ayyukan ibada, komai kankantarta, sai ta bata su. Allah Ya kare mu daga shirka!
Manufa ita ce, farkon abin da ake bukata shi ne kudurcewa da tabbatarwa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai (Allah) Mai gafara, Mai sa soyayya, Wanda Yana son bayinSa, Yana sa soyayya tsakanin bayinSa. Saboda haka a bauta maSa, Shi kadai da imani da gamsuwa ta yakini (sakankancewa da yarda), sannan da yi maSa da’a, kan cikakkiyar gaskiya da ikhlasi – tsarkake aiki gare Shi, Shi kadai (kada a hada kowa da Shi cikin bautar). Sannan kuma a bi ManzonSa (SAW), shi ma da gaskiya (a gaskanta shi) a cikin duk abin da ya ba da labari, a yi biyayya gare shi, gwargwadon iyawa, kan abin da ya umarta, kuma a nisanci duk abin da ya hana, ya yi kwabo a kansa.
Mu kwana nan.