Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, tare da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa, har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, yau za mu kai karshen hanyarmu, har mu tsaya bakin kofar Aljanna, muna jiran a bude mu shiga, insha Allah, muna bakin Allah Mai girma da daukaka. Mun kwana a karshen bayani na lamba ta shida a sauran sinadaran karasa tafiyar, sai mu je zuwa:
7. Sannan mu kiyaye hannunmu. Kada mu cutar da kowa da hannunmu, wajen duka ko kisa ko abin da ya yi kama da shi, musamman ma kananan yara, wadanda ya kamata a saisaita su a rayuwa don su girma su bi tsari na shari’a. Kada mu sa hannunmu mu dauki dukiyar wani, kada mu dauki kayan kowa, dukiyar haram. Kada mu yi amfani da hannunmu mu yi caca. Kada mu yi amfani da hannunmu mu rubuta abin da ba mu gani ba (zur), ko kuma wani abu batacce, ko karya. Ko a tes ne a wayarka, ka rubuta karya, ka ce, ‘ai wannan tes ne,’ … duk dai sunansa ka yi karya. Ba a cewa, ‘ai wannan rubutu ne,’…da ka yi da hannu da ka yi da baki duk daya ne. Tunda, misali yanzu idan kuka yi cinikin gida da wani, ka yi rubutu cewa, kai wane ka sayar wa wane gidan nan a kan kaza, ko abin da ya yi kama da haka, na rubutu, ai ba maganar baka ba ce, sai dai tana matsayinta ne. Duk wannan sai dai mutum ya ce zai yi jayayya, har ya kai ga ya sha ko ya kubuta a nan duniya. In ka kubuta a nan duniya, me ke nuna za ka sha ko ka kubuta a Lahira?
8. Sannan mu tsare kafafuwanmu! Kada mu tafi da su zuwa wurin wasan banza ko badil (batacce). Kada mu yi amfani da su mu kai su inda za su jawo mana wata fitina ko fasadi (barna) ko sharri. Ba a zuwa kallon hargitsi! Duk lokacin da ka ji wata rugumniya, to ka kula ka yi kaffa-kaffa, kada ka kai kanka inda za ka sha wuya, kana zaune a gidanka za ka ji yadda aka yi. Da yawa mutum yakan tafi wurin kallon wani abu, ya koma shi ake kallo, domin wanda ya aikata abin ma ya sulale, kai a zo a kama ka. Kada ka sake ka rika yin tawakkalin kuda, ka fada wa halaka kana ji kana gani! Allah Ya kiyaye mu!
9. Mu tsare alkawari da shaida da amana. Kada mu warware wani abu da aka kulla da mu na alkawari. Kada mu warware alwashin da muka yi. Kada mu ci amana. Duk abin da aka kulla da mu, to mu cika shi har zuwa karshensa, saboda Allah! Wajen shaida kuma kada mu yi shaidar zur (abin da ba mu ji ba mu gani ba, mu ce mun ji mun gani). In an ba mu amana kada mu yi yaudara game da ita, sai dai mu bayar da ita yadda take, yadda ya kamata a cikin mutunci da sanin ya-kamata!
10. Lallai mu tsare dukiyarmu. Kada mu wulakanta dukiyar da Allah Ya ba mu, lallai mu yi tattalinta. Kada mu wuce wuri wajen yin amfani da ita, kuma kada mu bar ta haka nan, ba mu jujjuya ta don ta karu. Misali, kada mutum don takamar yana da miliyan goma, ya koma ya yi zaman dirshan, yana bushasha da ita har ta komo miliyan daya. A’a, lallai ne ka samo hanyoyin da za ka habaka ta don ta karu! Tanaji babban al’amari ne a rayuwa, saboda haka sai a kula, amma fa kuma kada a yi rowa – a rika yin kyauta da sadaka da sauran ayyukan alheri, wadanda shari’a ta nuna, ta yarda da su.
11. Mu kiyaye iyali da ’ya’ya! Mu tsare mutuncinsu da jikunansu, musamman ma yara kanana. Duk abin da aka ga dalili a kansa cewa yaro zai iya ya ji ciwo a cikin gida ko a waje, lallai a tabbatar an kawar da shi, an kai shi inda ba zai kai gare shi ba. Kada a aje duk wani kayan jin rauni, kamar su wuka ko reza ko allura, musamman ma ta asibiti domin kada in ba kowa, yaro ya dauka ya tsira wa wani ya ce wai zai yi masa allura ne saboda ya ga ana yi a asibiti. Yaro abin da ya gani a aikace, sai ya ce shi ma zai kwatanta! Kada a aje magani inda zai ji mai dadi, ya dauki kwalbar gaba daya ya kwankwade. In an lura, har a jikin kwalaben magunguna ana rubuta cewa kada a aje inda yaro zai dauka. Saboda haka a lura da irin wadannan tsawace-tsawace.
Mu kiyaye iyali dangane da hankulansu – kada a bari su rika shaye-shayen kayan maye da gusar da hankali! A kula da akidarsu – kada a bari su zama karkatattu kuma batattu, wadanda ba su bin tafarkin sunnar Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam). Lallai a tabbatar suna kan wannan tafarki na akidar Ma’aikin Allah, mai tsira da amincin Allah, wadda ya karantar da sahabbansa har suka gama rayuwarsu a kanta.
Mu kula kuma mu kiyaye halayensu, mu kare musu duk abin da zai cutar da su a rayuwa, balle har mu bari ya bata musu rayukansu. Mu tunkude musu duk abin da zai jawo musu halaka a nan duniya, wanda har zai iya jawowa su kasance ’yan wuta a Lahira. Babu dadi a wayi gari ka auro mata ta haifi da, ka yi dalili da suka koma Lahira suka shiga wuta. Lallai idan ba a shiryar da su kan hanya madaidaiciya ba, to ai an ci amanarsu. Ka ga kuwa ashe dole ne a tsare wadannan abubuwa. Allah Ya tallafa mana!
Malam Aljaza’iriy ya ce to, jama’a, duk wanda aka zo da shi nan, bai sauka daga kan wannan hanya ba, to hanya ta zo karshe, yanzu mun iso kofar gida. Saboda haka, ya ku ma’abuta wannan tafiya, yanzu ga Aljanna nan mun iso, gidan aminci, sai ku kinkintsa, ku shisshirya, ku jira a ce ku shigo, bayan Manzannin Ubangijinku sun shiga, don su za su fara shiga. Daga nan ne kuwa sai sakon da suke dauke shi (su Manzannin) daga Mai ni’imtarwa, Mai karamci, Allah (Subhanahu Tabaraka Wa Ta’ala) ya zo, mai cewa ku shiga kawai alhalin kuna bakinSa.
A wannan ranar ce masu takawa za su yi murna! Ya Allah Ka sanya mu cikin masu takawa don kyautarKa da karamcinKa da falalarKa. Amincin Allah ya tabbata ga ManzanninSa, kuma dukkan yabo da godiya sun tabbata gare Shi, Ubangijin talikai!