Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, tare da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa, har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, yau mukalarmu tsokaci ne kan manuniyar hanyar zuwa Aljanna ga wanda Allah Ya nufa da bin ta (ita hanyar) har ya shige ta (ita Aljanna) din. Allah Ya sa muna cikin masu dacewa wajen bin wannan hanyar, har mu kai ga shiga Aljannar, amin.
Mukalar za ta gudana ne daga fassarar littafin da Shehun Malami, Abubakar Jabir Aljaza’iriy ya wallafa, mai suna: ‘Aljannatu Darul Abrar Waddariku Muwassalu ilaiha,’ kuma Malam Usman Almisriy ya karantar da shi, tare da yin wasu karin bayanai. Allah Ya saka musu da alheri, duniya da Lahira, amin. Ni kuma na rattaba shi a takarda, saboda kwadayin lada wajen yayata hanyoyin bin Allah da koyi da abin da dan aikenSa, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya kawo. Allah Ya ba mu dacewa mai amfani!
Tun farkon littafin dai, sai da aka yi bayanin yadda Aljannar take da irin abubuwan morewar da ke cikinta ta yadda duk wanda ya ji bayanan, babu shakka, zai kwadaitu ya shige ta. A karshen littafin ne aka shimfida yadda za a bi hanyar, har a kai ga shiga Aljannar.
Kullum abin da mutum zai ta roko shi ne, Allah Ya taimake shi ya rayu a kan Musulunci har iyakar rayuwarsa. Sannan sa’ar da mutuwa za ta zo (masa), ya mutu yana Musulmi, a karbe shi yana mumini. Idan aka je Lahira da wannan matsayi, to, duk matsalar da za a samu, insha Allahu, mutum zai tsallake (ya tsira).
Ga hanyar nan:
Hanyar sananna ce. Ba hanya ce wadda aka boye ba balle mutum ya wahala wajen neman inda da yadda take, kuma ita kadai ce hanyar, ba wata sai ita. Kuma duk wanda Allah Ya sa ya yi sa’a ya dace yana tare kuma yana kan wadannan abubuwa da za a ambata game da hanyar, to sai ya yi ta fata Allah Tabaraka wa Ta’ala Ya ba shi tabbata da daidaito a kanta. Ba wani wanda ya azurta, ko Allah Ya ba wata kyauta ko baiwa, wadda ta fi ta. Abin duniya duk da aka ba wani, matsayi ne ko dukiya ko wani abu daban dai, jarrabawa ce. Rasawar ma jarrabawa ce. Wanda ya fi kowa shi ne wanda ya ci jarrabawar. Saboda haka wanda aka ba, an ba shi ne don a yi masa jarrabawa. Wanda ba a ba shi ba, shi ma dai an yi masa haka ne don jarrabawa.
Ita duniya ana ba da ita ga wanda ake so da wanda ba a so. Kada a ga wani da matsayi na duniya ko wani abu, a dauka shi ne Allah Ya daukaka ko Ya zaba. Akwai bukatar a lura cewa akwai daukaka tabbatacciya, akwai kuma wadda take ta wahami da rudi. Yana yiwuwa wani ya hada biyun, wato Allah Ya ba shi a nan duniya, kuma Ya ba shi a Lahira. Wannan kuwa al’amari ne da ke Hannun Allah da Yake ba wanda Ya so. Wani kuma za a hana shi a nan duniya din har ya ga kamar ma shi hakan shi ne ya fi masa. Duk yadda ka ga halin da Allah Ta’ala Ya ajiye ka, to, (in ka gane) wannan halin shi ya fi maka, domin duk yadda kake son kanka, ko kusa ba ka kai yadda Allah ke sonka ba.
Allah Ya sa rahamarSa, guda dari ce, cas’in da tara na HannunSa, Ya dauki daya tak Ya sanya a cikin duniya gaba daya. Uwa, tausayin da take wa danta, duk a cikin dayan nan ne aka gutsura mata. Saboda haka Wanda ke da wannan, ai kuwa Ya fi sonka fiye da yadda kowa ke sonka. In ka ga ya ajiye ka a wani matsayi, to, hakan shi ya fi maka.
Yanzu sai kawai mu fara bayyana hanyar da abin da za a rike don a kai gaci.
Ita wannan hanya, kamar yadda aka ce, bayyananniya ce ba boyayyiya ba. Hanya ce shimfidaddiya, sanannniya, wadda aka saba bi, saboda haka ba ta da wahalar bi, domin bayin Allah masu yawa sun bi ta sun wuce. Shararrariya ce, sababbiya, wadda take da alamomin da mutum in ya bi ta, ba zai bace ba. Kai, hasali ma dai a samanta fitilu ne ta yadda ko’ina haske ne, balle a ce za a yi ta bundum-bundum wajen neman inda take.
Akwai bukatar a lurar da mai karatu cewa tafiyar tana da wahala, idan aka fara ta. Tafiyar tana da mataki-mataki har hudu, daya bayan daya. Shi ya sa za a ga, wasu da an fara tafiyar, sun sauka daga hanyar tun a matakin farko. Saboda haka sai a dage, a jajirce, kada a karaya ko a yi sake, har sai an kai bakin kofofin Aljannar, wadanda suke bubbude kawai. Allah Ya ba mu tabbata tare da cin nasarar kaiwa gare su, mu samu shiga ciki.
A tuna! Hakuri babban al’amari ne. Yayin da aka cije, aka daure, cikin sa’a guda sai a samu kyakkyawan sakamako. In kuma aka sare, aka gaza, shi ma cikin sa’a guda, sai ka ga an fadi. Saboda haka ku taho mu bi wannan hanya, wadda Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi wasallam), ya siffanta mana ita, a cikin fadinsa biyu: Farko ya ce, “Na bar ku a tsakiyar hanya, wadda take fara fat, wadda darenta kamar yininta ne, daidai yake, (ko ta ina kyau gare ta). Ba wanda zai karkata daga kan wannan hanya, sai wanda yake batacce.”
Don haka kada wanda ya sake ya sauka daga kan hanyar nan. Ku zo mu bi wannan hanya da Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya bari, wadda ba mai karkacewa (daga gare ta), sai halakakke. Allah Ya kiyashe mu da kasancewa cikin halakakku!
Bayan nan ya kara cewa, “Dukkanku za ku shiga Aljanna, sai wanda ya ki (ya ce ba ya so).”
Sai sahabbai suka tambaye shi, “Wa zai ki kuwa (ya ce ba ya son shiga Aljanna), ya Rasulallah?”
Sai ya ce, “Duk wanda ya yi mini biyayya, (ya bi abin da na karantar), ya shiga Aljanna; wanda kuwa ya saba mini, (wannan ya ce) ba ya son Aljanna (kawai, kai-tsaye).
Mu kwana nan sai mako na gaba, in Allah Ya kai mu, za mu ci gaba. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatu!