Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, Wanda Ya sanya wa bayinSa (Musulmi) kyakkyawan tsarin rayuwa. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga BawanSa, ManzonSa, Muhammad, wanda aka aiko a matsayin jinkai ga halittu gaba daya, tare da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsa har zuwa Ranar karshe.
Bayan haka, tsokacin makon jiya na (3) ba na (2) ba, kuskure aka yi, to, yau ga ci gaba. Muna fata Allah Ya sa ana amfana da abin da ake karantawa kuma ana aiki da shi don a samu tsira wajen Allah.
Shi Musulmi na kwarai yana sadar da zumuntarsa koda abokin zumuncin nasa ba Musulmi ba ne, saboda irin saukin kai da mutumtakar da Musulunci yake da shi. Abdullahi dan Amru dan Aas, (Allah Ya yarda da su), ya ce, “Na ji Manzon Allah yana cewa, “Iyalin su wane da wane ba abokaina ba ne; abokaina su ne Allah da duk wadanda suka yi imani (muminai), amma su (wadancan iyalai) suna da dangantaka da ni, wadda zan lura da ita kuma in cika ta.” (Buhari da Muslim ne suka ruwaito Hadisin).
Haka nan a yayin da aka saukar da ayar, “Kuma ka yi gargadi ga danginka mafiya kusanci.” (Surar Shu’ara’ 26, aya ta 214), sai Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya tara kuraishawa, ya yi kira, “Ya ku ’ya’yan gidan Abdus Shams, ya ’ya’yan gidan Ka’abu dan Lu’ayyu, ya ’ya’yan gidan Murratu dan Ka’abu, ya ’ya’yan gidan Abdul Manaf, ya ’ya’yan gidan Hashim, ya ’ya’yan gidan Abdul Muddalib! Ku tseratar da kawunanku daga wuta; ya Fatima! Ki tseratar da kanki daga wuta. Ba zan iya kare ki da komai daga azabar Allah ba; (dukkanku) akwai igiyar zumunci tsakaninmu, wadda zan kula da ita kuma in tsare ta.” (Imam Muslim ne ya ruwaito shi).
Zuciyar Musulmin kwarai cike take da shauki na tausayi da kauna wajen kyautata dangantakarsa da ’yan uwansa koda su ba Musulmi ba ne. Misalin da Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya bayar an kwatanta shi da gona, wadda ake kula da ita, ana gyara ta a kai-a kai, ta yi yabanya ta fitar da amfani mai yawa, ganinta zai dadada rai, to haka zumunta take domin tana haifar da soyayya da kaunar juna ta samar da zaman lafiya da kwaciyar hankali. Kamar haka ne idan aka wofintar da ita, ba a shayar da ita, sai ta bushe, ta kekashe, wato idan aka yanke zumunta, sai kiyayya da tashin hankali da rashin zama lafiya su tohu.
Irin wannan kyakkyawar karantarwa ce ma ta sa Umar dan Khaddab, (Allah Ya yarda) da shi, ya cire rigar da Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya aika masa da ita, ya ba wani dan uwansa, wanda yake mushriki kyauta, kamar yadda Hadisin da Buhari da Muslim suka ruwaito, ya nuna.
Martabar Musulunci ke nan da rungumarsa ga kowa da kowa ta fuskar sanin matsayi da martabar mutum, wajen nuna kyakkyawar dabi’a da kauna. Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda shi ne aka aiko da Musulunci ya kasance jinkai ga al’ummar duniya, kamar yadda Alkur’ani ya nuna mana, a aya ta 107, cikin sura ta 21 (Ambiya’) wato, “Kuma ba Mu aike ka ba face domin wata rahama ga talikai.” Da kuma abin da shi Ma’aikin Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Ba a aiko ni ba, sai don kawai in cika kyawun hali da dabi’a.” (Muwadda Malik).
Musulmi na kwarai ya san ma’anar rike zumunci da sadar da shi a duk lokacin da bukatar haka ta taso, musamman da yake ya san cewa wani yanki ne na addininsa. Yana sane da cewa lamarin bai tsaya a kan bayar da kudi ba. Akwai biyan juna –abin da Bahaushe yake cewa “Zumunta a kafa take,” saboda haka sai ana ziyartar juna, ana watsa kaunar juna da tausasawa da jinkai da ba juna shawarwarin yadda za a warware wadansu matsaloli na rayuwa da shiryarwa ga abin da yake da amfani da sakin fuska. Kai da dai yin duk sauran abubuwan da za su haifar da tabbatuwar dankon soyayya a tsakanin ’yan uwa.
Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Ku rike igiyar zumunci koda da gaisuwar sallama ne (wato a rika ce wa juna ‘Assalamu alaikum’ da sakakkiyar fuska).” Imam Albazzar ne ya ruwaito shi daga Abdullahi dan Abbas, da isnadoji masu yawa wadanda ke tallafa wa juna.
A karshe, Musulmi na kwarai ba ya yankewa daga danginsa koda su sun yanke daga gare shi, saboda ya san muhimmancin zumunci a Musulunci. Duk wanda yake tsare zumuntarsa, saboda Allah, ba ya neman lallai a yi masa kamar ko fiye da yadda yake yi wa danginsa. Sada zumuntarsa ba biki ba ce, balle ya yi tunanin a mayar masa yadda ya yi ko ma fiye. A kan haka ne ma Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Duk wanda yake rike da zumunta don kawai danginsa suna biya shi, ba mai zumunci ne na gaskiya ba. Wanda yake zumunci na gaskiya shi ne wanda koda danginsa sun yanke masa, to shi yana biyar su.” (Imamul Buhari ne ya ruwaito shi).
Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya bayar da karsashi da shawara don karfafa kyautatawa da hakuri da yafiya da juriya a zuciyar wanda yake kokarin sadar da zumunci, alhali danginsa suna juya masa baya a kan haka. Mai yin haka, Allah Yana tare shi. Wani mutum ya je wajen Annabi, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Ya Manzon Allah, ina da dangi wadanda nake kyautata musu, amma suna juya min baya, suna cutar da ni.” Annabi (SAW) ya ce, “In dai yadda ka ce haka kake, to kamar kana zuba musu turbaya mai zafi ne a cikin bakunansu. Allah Zai ci gaba da taimakonka, matukar ka ci gaba a yadda kake yi.” (Imam Muslim ne ya ruwaito shi).
Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Igiyar zumunta a rataye take da Kursiyyu, tana cewa, ‘Duk wanda ya sadar da ni, ya kula da ni, ya taimake ni, Allah Zai taimake shi; wanda duk ya yanke ni, Allah Zai yanke shi.” (Buhari da Muslim ne suka ruwaito shi). Saboda haka jama’ar musulmi, mu sada zumuncinmu, mu rike shi da kyau don mu samu taimakon Allah.
Allah Shi ne Mafi sani, muna rokonSa Ya ba mu dacewa.
Wassalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuh!