Allah Ya yi wa tsohuwar Ministar Mata, Amina-Jummai Alhassan, wadda aka fi sani da Mama Taraba rasuwa.
Bayanan sun ce Jummai Alhassan ta rasu ne a wani asibiti a birnin Alkahira na kasar Masar tana da kimanin shekara 62 a duniya.
- ’Yan fashi sun tare motar banki, sun daka wa kudin cikinta wawa
- Bikin Sallah: An dakatar da kilisa da hawan Sallah a jihar Neja
Wani tsohon mai magana da yawun Maman Taraba, Suleiman Dantsoho, ya ce Allah Ya yi mata cikawa ne a ranar Juma’a.
Mama Taraba fitacciyar ’yar siyasa ce a Jihar Taraba, inda a shekarar 2015 ta yi takarar gwamna karkashin jam’iyyar APC.
Shugaba Buhari ya nada Mama Taraba Ministar Harkokin mata, bayan Gwamna mai ci Dariusa Ishaku ya kayar da ita a zaben.
Daga baya a 2018 ta sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP, bayan jam’iyyar APC ta hana ta tsanayawa takara a zaben 2019.