Ivana Trump, tsohuwar matar tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump ta mutu tana da shekara 73.
Marigayiyar dai ita ce matar Trump ta farko wacce ta haifa masa ’ya’ya uku.
- An gano kabari mai mutum 8,000 da dakarun Hitler suka kashe a Poland
- Shugaban Sri Lanka ya ajiye aiki bayan ya tsere zuwa Singapore
Donald Trump din ne ya tabbatar da mutuwar tata da maraicen Alhamis.
Trump ya wallafa a shafukansa na sada zumunta cewa, “Mutuniyar kirki ce, mai kyan hali kuma mace ta gari, wacce ta taka muhimmiyar rawa a rayuwata.”
An dai haife ta ne a Jamhuriyar Czech, kuma ta auri tsohon Shugaban na Amurka a shekarar 1977.
Sai dai shekara 15 bayan yin auren nasu wato a 1992, sun rabu.
Sun haifi ’ya’ya uku tare – Trump Karami, Ivanka da kuma Eric.
Duka su biyun dai sun yi fice a birnin New York a shekarun 1980 zuwa 1990, kuma batun rabuwar aurensu na daga cikin batutuwan da mutane suka fi tattaunawa a lokacin.
Amma bayan rabuwar tasu, Misis Trump ta kama sana’ar sayar da kayan kwalliya da sutturu da sarkoki ka’in da na’in.