An kama wata tsohuwar mai shekara 83 bisa zarginta da koya wa kyawoyinta satar sarkuna da wasu abubuwa masu daraja daga gidajen makwabta.
’Yan sandan Columbus, babban birnin Jihar Ohio na kasar Amurka ne suka kama tsohuwar, kuma sun fara gudanar da bincike.
Tsohuwar mai suna Ruth Gergson, tana fuskantar zargi ne bayan makwabta sun kai kara ofishin ’yan sanda cewa ana sace musu kananan kayayyakinsu da suka ajiye a gida, kuma suna zargin kyanwoyin Ruth 65 da laifin satar.
Da yawa daga cikin wadanda suka kai karar sun ce, kafin a musu satar kayan, suna ganin kyanwoyin Ruth a gidansu, sdaga bisani kuma sai su ga wani abu ya bace musamman abubuwa masu kyalli kamar kwanukan cin abinci da sarkuna da sauransu.
Da ’yan sanda suka fara bincike, sai suka yi mamakin abin da suka gane wa idonsu. Shugaban ’Yan sanda Columbus, Kim Jacobs ya ce, kyanwoyin suna shiga gidajen makwabta, jim kadan sai su fito da abubuwa musamman masu daukan ido.
“Tsohuwar tana kama da Fagin a fim din Oliber Twist, amma sai dai tana amfani ne da kyanwoyin ne maimakon ’ya’yanta. A cikin awa uku da ’yan sanda suka yi sintiri a yankin, sun gane wa idonsu yadda kyanwoyin suke dauko kayan da ake zargi ana sacewa.”
Da haka ne ’yan sanda suka shiga gidan Ruth domin bincike. Bayan sun bincika, sai suka gano sarkuna na kimanin Dala dubu 650 (kimanin Naira miliyan 234) da wasu karafa masu kyau da sauransu.
Daga baya tsohuwar ta tabbatar da cewa ita take koya wa kyawoyin yadda za su yi sata, domin a cewarta, “Dole su nemo abin da za su ci.”
’Yan sandan suna zargin cewa kyanwoyin Ruth sun yi sata a gidaje sama da dubu 5 a yankin.