✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohowa ta yanke jiki ta fadi a layin cirar kudi a banki

Wata tsohuwa da ta je cire kudi a banki ta yanke jiki ta fadi a kasa a safiyar ranar  Alhamis.

Wata tsohuwa da ta je cire kudi a banki ta yanke jiki ta fadi a kasa a safiyar ranar  Alhamis.

Lamarin ya faru ne bayan mutane sun yi dafifi a wani reshen bankin First Banki da ke Jihar Oyo, tun da sanyin safiya domin bin layi cirar tsabar kudi.

Bayan mutanen sun yi layi suna jiran a bude bankin, da misalin 8:50 na safiya wani jami’in tsaron bankin ya bukaci wasu daga cikinsu su shiga cikin harabar, inda aka tanadar wa kwastomomi kujeru.

Sai dai an yi rashin sa’a tsohuwar ba ta samu shiga ba har aka rufe kofar, kasancewar sabuwa zuwa ce.

Bayan ta farfadowarta sai ta fashe da kuka, inda ta bayyana cewa tana fama da matsanancin rashin lafiya ne kuma tana bukatar kudi.

An yi katari, jami’an tsaro sun zo sun taiamaka watar, wadda ta kasa tafiya.