Tsohon Shugaban Hukumar Wakafi ta Shi’a (Shia Waqf) na yankin Uttar Pradesh da ke kasar Indiya, Wasim Rizvi, ya koma addinin Hindu (da aka fi sani da Sanatan Dharma) a ranar Litinin din makon jiya.
Ya ba da hadayar madara a Shiva Linga, wani wurin bauta na mabiya addinin Hindu a zaman wani bangare na shiga adddinin, inji jaridar Hindustan Times.
- Saudiyya ta aike da jiragen kayan tallafi zuwa Afghanistan
- Yadda wutar lantarki ta kashe barawon wayar wuta a Gombe
An gudanar da bikin ne da misalin karfe 10.30 na safe, a gaban babban limamin wurin bautar na Dasna Devi Temple, Narsinghanand Saraswati, inji kafar labarai ta Livehindustan.
An yi ta rera wakoki yayin da Rizvi ya bar addinin Musulunci ya koma addinin Hindu.
A yanzu za a hada shi da al’ummar Tyagi, kuma sabon sunansa ya zama Jitendra Narayan Singh Tyagi.
Bayan bikin, Rizvi ya bayyana Sanatan Dharma a matsayin addini mafi tsafta a duniya.
Ya ce ya zabi ranar 6 ga Disamba ce domin ya koma addinin Hindu don a wannan rana ce aka rushe Masallacin Babari a 1992.
“Zan yi wa addini Hindu aiki daga yau. Kuri’ar Musulmi ba ta zuwa ga wata jam’iyya. Suna kada kuri’unsu ne kawai don kayar da ’yan Hindu,” Rizvi ya shaida wa Livehindustan.
Rizvi ya samu kansa a tsaka mai wuya bayan ya wallafa wani littafi mai suna ‘Muhammad’ a watan jiya.
Malamai da yawa a Uttar Pradesh sun yi Allah wadai da bangon littafin da ke nuna wani mutum da mace tsirara-tsirara. Sun kuma zargi Rizvi da yin kalamai cin zarafin Annabi (SAW).
Wasu daga cikin kungiyoyin addini da suka hada da All India Shi’a Personal Law Board (AISPLB), sun bukaci ya janye littafin, yayin da wadansu suka tunkari gwamnatin Lardin Uttar Pradesh suna neman a kai su kotu kan lamarin.
An fitar da littafin a ranar 4 ga Nuwamba a gidan bauta na Dasna Devi da ke Ghaziabad a gaban Narsinghanand Saraswati; Musulmi ’yan Sunni ne sun la’anci littafin.
Daga baya Wasim Rizvi ya fitar da wata sanarwa inda ya ce yana fuskantar barazana ga rayuwarsa saboda rubuta littafin da kuma sukar ayoyi 26 na Alkur’ani Mai girma da ya yi.