✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon Shugaban PDP a Kano ya sauya sheka zuwa NNPP

Shehu Wada Sagagi da PDP da ke bangarensa sun koma Jam'iyyar NNPP

Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Kano, Shehu Wada Sagagi, tare da sauran jagororin da ke bangarensa, sun koma jam’iyyar NNPP.

Sagagi da magoya bayan sa sun sauya sheka ne a ranar Lahadi a hannun shugaban NNPP na kasa Bishop Isaac Idahosa yayin yakin neman zaben jam’iyyar da aka gudanar a Kano.

Da yake jawabi yayin yakin neman zaben, Sagagi ya ce ya koma jam’iyyar ne tare da shugabannin zartaswar PDP 36, da na kananan hukumomi guda 700, da fiye da 8,000 daga mazabu, sai daliget na kasa guda 44, da na mazabu 1,452.

Idan za a iya tunawa dai a shekarar 2022 ne Sagagin ya ce ba zai bi mai gidansa, Rabiu Musa Kwankwaso zuwa NNPP ba, inda ya zauna ya rike shugabancin PDP a Jihar Kano.

Wannan ne ya sa wasu daga cikin ’ya‘yan jam’iyyar zargin cewa Kwankwason Sagagi yake yi wa aiki.

Sai dai a jawabinsa na sauya sheka, Sagagi ya ce sun fice daga PDP ne saboda hana dimokuraɗiyya yin aikinta, da kuma nuna bangaranci a siyasar cikin gida.