✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon Shugaban Ghana Jerry Rawlings ya rasu

Rawlings ya rasu yana da shekara 73 bayan fama cutar coronavirus.

Rahotanni daga kasar Ghana na cewa tsohon shugaban kasar Jerry Rawlings ya rasu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus.

Rawlings ya rasu yana da shekara 73 bayan jinya a Asibitin Koyarwa na Korle-Bu da ke birnin Accra, babban birnin kasarsa a safiyar Alhamis.

Marigayi Rawlings shi ne shugaban da ya fi dadewa a gadon mulkin kasar, daga 1981 zuwa 2001.

Ya fara jagorantar kasar ne a mulkin soja bayan ya jagoranci juyin mulki a 1981; daga baya a 1992 ya zama zababben shugaban mulkin farar hula a jamhuriya ta hudu.

Ana kallo, wanda shi ne ya kafa jam’iyyar NDC a matsayin wanda ya ceto Ghana daga mawuyacin halin da ta shiga a lokacin gwamnatin da ta gabace shi.