Tsohon Sakataren Harkokin wajen Amurka, Janar Collin Powell, kuma baki na farko da ya rike wannan mukamin, ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.
Janar Powell wanda gwarzon yaki ne da ya taka rawa wajen mamaye kasar Iraqi a shekarar 2003, ya rasu a ranar Litinin sakamakon cutar Coronavirus.
- Squid Games: Fim din Netfilx mafi shahara a duniya
- Mahara sun bindige mutum 65 a asibiti da kasuwar Sakkwato
Iyalansa da suka bayyana rasuwar cikin wani sako a shafin Facebook, sun ce ya kammala karbar dukkanin allurar rigakafin Coronavirus, amma hakan bai hana ta yi ajalinsa ba.
Bayanai sun ce ya kasance daya daga cikin manyan mutane a Amurka da suka riga mu gidan gaskiya sakamakon kamuwa da cutar.
A cewar iyalansa, “mun rasa Uba, Miji kuma Kaka na gari mai kishin kasa wanda ya bayar da gudunmuwa wajen kare martbatar Amurka.”
Bayan ja gaban da ya yi wa dakarun soji wajen samun nasara a yakin Gulf a shekarar 1991, Powell ya shahara tare da samun girmamawa da har aka nemi ya tsaya takara domin zama Shugaban Amurka bakar fata na farko a tarihi.
Sai dai daga bisani ya yanke shawarar kin tsayawa takara kuma ya sauya sheka daga jamiyyarsa ta Republican domin goyon bayan takarar tsohon Shugaban Amurka, Barack Obama.
Tsohon shugaban kasa George W. Bush ya bayyana Powell a matsayin gwarzon Amurka, abin misali a kasar da kuma wanda za’a ci gaba da bada tarihin sa, lokacin da ya gabatar da sunansa domin zama Sakataren harkokin waje a shekara ta 2000.
A shekarar 2003, Janar Powell ya shaida wa Majalisar Dinkin Duniya takaicin sa na mamaye Iraki wadda aka zarga da mallakar makamin nukiliya.
A wata hira da ya yi da tashar ABC News a shekarar 2005, Janar Powell ya bayyana mamayar Iraki a matsayin tabon da zai ci gaba da rayuwa da shi har mutuwarsa.