✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Sakataren NEPU MK Ahmed ya rasu

Ya rasu ya bar 'ya'ya 30 da jikoki masu tarin yawa.

Tsohon Sakataren Gudanarwa na Jam’iyyar NEPU, Alhaji MK Ahmed, ya rasu yana da shekara 96 a duniya.

Daya daga cikin ’ya’yansa, Suleiman Ahmed ne ya shaida wa manema labarai cewa mahaifinsu ya rasu a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), bayan ya sha fama da jinya.

Ya ce mahaifin nasu wanda ya rasu a safiyar ranar Asabar, ya bar mata guda daya da ’ya’ya 30 da kuma jikoki da dama.

A hirarsa ta karshe da Aminiya a shekarar 2018, marigayin wanda dan siyasa ne ya bayyana yadda aka nada shi Sakataren Yada Labarai na NEPU bayan ya yi aiki tare da marigayi Malam Aminu Kano a matsayin Babban Sakatarensa kafin ya zama Sakataren Gudanarwa na jam’iyyar a shekarar 1961.

Marigayi MK Ahmed shi ne ya kafa Kungiyar Jin Dadin Alhazai ta Najeriya a shekarar 1961 kuma ya zama Sakataren kungiyar.

Marigayin wanda shi ne mawallafin littafin “Chronicle of NEPU/PRP,” ya yi aiki a kungiyoyi daban-daban na gwamnati da masu zaman kansu kamar Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Najeriya, TCN, Hukumar Wutar Lantarki ta Kasa (NEPA) da sauransu.

Ya samu lambar yabo ta Kasa ta MFR, a 2003.