✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon Sakataren Gwamnati kuma Shugaban Ma’aikatan Edo ya rasu

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Jihar Edo kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar, Dokta Simon Imuekemhe ya rasu.

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Jihar Edo kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar, Dokta Simon Imuekemhe ya rasu.

Ya rasu da sanyin safiyar Alhamis yana da shekaru 66 bayan gajeruwar rashin lafiya da ya sha fama da ita.

Dokta Simon wanda dan asalin yankin Ikabigbo ne a Karamar Hukumar Etsako ta Arewa a jihar Edo.

Kafin rasuwarsa, marigayin kwararren likita ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan kuma daya daga cikin shugabannin masu karbar haraji na gwamnatin Jihar Edo.

Marigayin ya taba zama tsohon Sakataren Gwamnatin jihar zamanin mulkin tsohon gwamnan, Kwamared Adams Oshiomhole.

Kazalika, ya taba zama Shugaban Ma’aikatan Jihar a zamanin Gwamna Lucky Igbinedion.