Allah Ya yi wa tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya na Laftanar-Janar Jeremiah Useni, rasuwa.
Janar Jeremiah Useni, wanda yakasance ministan Abuja daga 1993 zuwa 1998, ya rasu yana da shekaru 82 bayan fama da doguwar jinya.
Gwamnatin Jihar Filato, mahaifarsa, ta sanar da rasuwar ta hannun Gyang Bere, kakakin Gwamna Caleb Mutfwanng, inda ya bayyana mutuwar a matsayin babbar asara ga Najeriya.
Ya bayyana cewa rasuwar ta shafi ba iyalan mamacin kaɗai ba, ta shafi rundunar Sojin Najeriya da Jihar Filato da ma ƙasa baki ɗaya.
- Dogo Giɗe ya kashe ’yan Boko Haram 20 ya ƙwace makamansu
- NAJERIYA A YAU: Matakan Samar Da Abinci A Kan Farashi Mai Rahusa A Najeriya
A nasa saƙon ta’aziyyar, Ministan Babban Birnin Tarayya, Ezenwo Nyesom Wike, bayyana rasuwar Janar Jeremiah Useni a matsayin faɗuwar babban bango abin jingina.
Marigayi Jeremiah Useni ya kasance Ministan Babban Birnin Tarayya a zamanin mulkin sojin Marigayi Janar Sani Abacha.
Wike ta hannun kakakinsa ya bayyana, cewa ba za a taɓa mantawa da gudunmawar Marigayi Janar Jeremiah Useni ba, musamman wajen ci-gaban da ya kawo wa Babban Birnin Tarayya a lokacin da yake minista.