✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon Mataimakin Gwamnan Zamfara ya koma PDP

Wakkala ya koma PDP ne saboda na mayar da su saniyar ware a jam’iyyar APC.

Tsohon Mataimakin Gwamnan Zamfara, Ibrahim Wakkala Muhammad ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP mai mulki a jihar.

Wakkala wanda ya yi mataimaki ga tsohon Gwamna Abdulaziz Yari daga 2011 zuwa 2019 ya bayyana hakan ne a Gusau babban birnin jihar, bayan ganawa da manyan magoya bayansa.

Wakkala ya ce, “Duk da kasancewarmu cikakkun ’ya’yan kungiyar G8, bayan rikicin da muka samu da jam’iyyar APC a 2019, amma ba a ci gaba da daukar mu masu muhimmanci a jam’iyyar ba.

“Ina son sanar da jama’a cewa daga karshe na sauya sheka daga APC na koma PDP tun daga matakin mazabata ta Madawaki da ke Karamar Hukumar Gusau,” inji shi.

Wakkala ya kara da cewa ya yanke hukuncin ne tun lokacin da wasu suka mayar da jam’iyyar APC ta zama ta ’yan amshin shata.

Ya ce tun kafuwar gwamnatin Bello Matawalle ya fara aikin ba da shawara, musamman a kan abubuwan da suka shafi harkar tsaro.

“Na amince da shiga PDP saboda tayin da gwamna ya min, kuma na yarda saboda ci gaban jihar Zamfara,” inji tsohon Mataimakin Gwamnan.