✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Mataimakin Gwamnan Kogi Patrick Adaba ya rasu

Patrick Adaba shi ne ya yi wa Prince Abubakar Audu mataimakin gwamna bayan samun nasara a Zaɓen 1999.

Tsohon Mataimakin Gwamnan Kogi, Cif Patrick Adaba ya riga mu gidan gaskiya.

An ruwaito cewa Cif Adaba wanda ya shafe shekaru 78 a doron ƙasa ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya a Abuja.

Wata majiya daga iyalansa ta ce tsohon Mataimakin Gwamnan ya rasu ne cikin daren ranar Lahadi.

Cif Patrick Adaba shi ne ya yi wa Prince Abubakar Audu mataimakin gwamna bayan samun nasara a Zaɓen 1999.

Tsohon Mataimakin Gwamnan wanda ya fito daga Ƙaramar Hukumar Adavi da ke Jihar Kogin, ƙani ne ga tsohon Darekta Janar na Hukumar Kula da Kafofin Watsa Labarai (NBC), marigayi Tom Adaba wanda ya rasu a watan jiya na Fabarairu.

Majiyar ta ce za a binne gawar marigayi Patrick Adaba a Abuja, inda aka binne yayan nasa.