Tsohon kociyan Paris St-Germain Christophe Galtier ya maye gurbin Hernan Crespo a matsayin kocin ƙungiyar Al-Duhail ta Qatar.
Galtier, mai shekara 57, ya lashe gasar Ligue 1 da PSG a kakar wasa da ta wuce amma ƙungiyar ta yanke shawarar sallamarsa inda ta maye gurbinsa da tsohon kocin Barcelona Luis Enrique a watan Yuli.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Kawo Lalacewar Tarbiyya A Wannan Zamani
- Majalisa ta bukaci gwamnati ta kafa hukumar kayyade farashin kayayyaki
A watan Disamba ne za a gurfanar da Bafaranshen gaban kotu, bayan wani bincike da aka yi kan zargin wariyar launin fata a lokacin da ya ke riƙe da mukamin kocin ƙungiyar Nice.
‘Yan sanda sun yi masa tambayoyi a watan Yuni kuma ya musanta zargin.
Galtier ya maye gurbin tsohon dan wasan Chelsea da Argentina Crespo, bayan ɗan wasan mai shekaru 48 ya raba gari da Al-Duhail ranar Laraba.
Ɗan Ƙasar Faransa Galtier ya taɓa zama gwarzon kocin Ligue 1 har sau uku kuma ya lashe babban gasar ta Faransa da Lille da kuma PSG.
Muƙamin da ya karɓa a Al-Duhail shi ne aikinsa na farko da zai yi a wajen Faransa kuma ya gaji tawagar da ta ƙunshi tsohon ɗan wasan Liverpool da Aston Villa, Philippe Coutinho.