✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon Kakakin Shugaba Buhari Malam Wada Maida ya rasu

Tsohon Shugaban Kamfanin Dillancin Labaru na Najeriya ya rasu da misalin 10.00 na dare

Tsohon Sakatare Yada Labarai na Shugaba Buhari kuma Shugaban Kwamitin Amintattun Peoples Daily Malam Wada Maida ya riga mu gidan gasikya.

Marigayi Wada Maida wanda tsohon Manajan Darektan Kamfanin Dillancin Labaru na Najeriya (NAN) ne ya rasu ne da misalin 10.00 na dare.

Iyalansa sun tabbatar da rasuwar tasa a Abuja bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a ranar Litinin 17 ga Agusta, 2020.

A ranar ce kuma ya dawo daga Jihar Katsina inda ya je domin yi wa wani abokinsa ta’aziyar rasuwar matarsa wadda ta rasu a makon jiya.

Mamacin na daga cikin masu hannun jari a kamfanin Media Trust Limited, masu jaridun Aminiya da Daily Trust da Tambari da Kilimanjaro da sauransu.

Kafin rasuwarsa, Wada Maida shi ne Shugaban Kwamitin Amintattu na NAN kuma dan Kwamitin Amintattu na Kungiyar ‘Yan Jarida ta Duniya.

A watan Maris din 2020 ya yi bikin cika shekara 70 a duniya.