Tsohon Gwamnan Jihar Yobe, Sanata Bukar Abba Ibrahim, ya rasu bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Gwamnan farar hula na farko a jihar, ya rasu yana da shekara 75 a duniya.
- INEC ta dakatar da jami’inta kan batan sakamakon zabe a Filato
- PDP ta doke APC a zaben cike gurbin Birninkudu/Buji
Rahotanni sun bayyana cewa, ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Makkah na kasar Saudiyya a ranar Lahadi.
Marigayin, ya yi gwamna daga watan Janairu 1992 zuwa Nuwamba 1993 a lokacin Jamhuriya ta uku.
An sake zabar shi sannan aka rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu 1999, inda ya yi wa’adi biyu a karkashin Jam’iyyar ANPP.
Daga baya Bukar Abba ya zama Sanata mai wakiltar Yobe ta Gabas a 2007 zuwa 2019.
Marigayin ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya 17 da jikoki da dama.
Ya kasance miji ga tsohuwar Ministar Harkokin Kasashen Waje, Khadija Bukar Abba Ibrahim.
Daya daga cikin mataimakansa Yusuf Ali, ya shaida wa Aminiya cewa, marigayin ya rasu bayan ya sha jinya a asibitin da ke Saudiyya.
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya jajanta wa iyalan mamacin kan rashinsa.
Wannan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Mamman Muhammad, ya fitar a ranar Lahadi.
Ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga gwamnati da al’ummar jihar baki daya.
“Wannan babban rashi ne a gare mu, muna fatan Allah (SWT) Ya gafarta masa kurakuransa, Ya sanya shi a Aljanna Firdaus” in ji Buni.