✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta doke APC a zaben cike gurbin Birninkudu/Buji

Adamu Yakubu ya lashe zaben cike gurbin ne da kuri'u 43,053

Dan takarar Jami’yyar PDP, Adamu Yakubu ya lashe zaɓen cike gurbin dan majalisar Tarayya mai wakiktar mazabar Birninkudu/Buji daga Jihar Jigawa.

Baturen zaben, Farfesa Ahmad Baita Garko said ya sanar cewa Adamu Yakubu ya lashe zaben cike gurbin ne da kuri’u 43,053.

Babban abokin adawansa, Da’u Magaji Aliyu na APC kuma ya zo na biyu da kuri’u 42,544.

Sauran abokan wadanda suka tsaya takara sun samu kuri’u kamar haka:

Ali Abdullahi Umar (NNPP) — 1,106

Isa Ado (ADP) — 170

Kamalu Usaman (ADC) — 81

Abdullahi Buhari (SDP) — 62.

Zaben cike gurbin na ranar Asabar dai ya gudana cikin lumana kuma ba tare da wata matsalar tsaro ba.