Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar PRP na Kasa, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya rasu.
Alhaji Balarabe Musa shi ne dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PRP a zaben 2003 kuma ya rasu ne yana da shekara 84 sakamakon rashin lafiya.
“Alhaji Balarabe Musa ya rasu. Allah Ya gafarta masa Ya sa Aljannar Firdaus ce makomarsa,” inji Shehu Sani tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya kuma makusancin mamacin a shafinsa na Twitter.
Iyalan mamacin sun ce za a yi jana’izarsa bayan Sallar La’asar a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna a ranar Laraba 11 ga watan Nuwamba, 2020.
A shekarar 1979 ne aka fara zaben Alhaji Balarabe Musa ya zama Gwamnan Kaduna wanda a watan Yunin 1981 Majalisar Dokokin Jihar ta tsige shi ya kuma zama gwamnan na farko da aka tsige a Najeriya.
A watan Agustan 2010 marigayin ya yi murabus daga harkokin siyasa ya kuma sauka daga kujerarsa ta Shugaban PRP na kasa saboda rashin lafiya.
Ana kallon marigayin dai a matsayin dan gaba-gaba wajen yakar gwamnatin mulkin soja ta marigayi Janar Sani Abacha.