An zabi Gilbert Houngbo, tsohon fira ministan kasar Togo a matsayin shugaban kungiyar Kwadago ta Duniya, wanda zai kasance dan Afirka na farko da zai jagoranci kungiyar da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya.
Bayan zagaye na biyu na kada kuri’a, kwamitin gudanarwar kungiyar ya zabi Gilbert Houngbo, a matsayin sabon shugaban da zai gaji dan kasar Birtaniya Guy Ryder, wanda ya yi murabus a karshen watan Satumban 2021 bayan shafe shekara 10 yana aiki.
- Balaraba Ramat Yakubu: Raina kama ka ga gayya
- Matashi ya jefa tsohuwa mai shekara 80 cikin rijiya a Kano
An zabi Houngbo ne daga cikin ’yan takara biyar bayan samu cikakken goyon baya daga bangarori daban-daban duk da juya bayan da kungiyar Tarayyar Afirka ta yi mishi.
Gilbert Houngbo, ya rike mukamai da dama karkashin hukumomin Majalisar Dinkin Duniya kama daga daraktan kudi a Hukumar Raya Kasashe da mataimakin babban darakta na kungiyar da ya samu shugabancinta yanzu a 2013 zuwa 2017.
Abokan takararsa sun hada da tsohon Ministan Kwadago na Faransa, Muriel Penicaud da tsohuwar Ministar Harkokin Wajen Korea ta Kudu, Kang Kyung-wha, da fitaccen dan kasuwar Afirka ta Kudu Mthunzi Mdwaba, sai kuma mataimakin kungiyar kwadagon Greg Vines daga kasar Australia.