Zakaran duniya a fagen kwallon kafa a 1974, Franz Beckenbauer ya mutu yana da shekara 78 a duniya.
Hukumar Kwallon Kafar Jamus (DFB) ce ta sanar hakan a ranar Litinin.
- An tura matashi gidan yari kan yi wa jaririya fyade
- Manyan mata 10 da badakala ta dabaibaiye kujerunsu
Beckenbauer ya bar kyakyawan tarihi ta fanin kwallon kafa, inda ya samar da ci gaba mai tarin yawa.
Beckenbauer, ya jagoranci Jamus wajen lashe Kofin Duniya a shekarar 1974.
Iyalinsa sun tabbatar da rasuwarsa a wata sanarwa da Kamfanin Dillancin Labaran Jamus DPA ya fitar.
“Cikin bakin ciki muna sanar da rasuwar mijina, mahaifinmu, Franz Beckenbauer, ya rasu a kusa da iyalinsa a ranar Lahadi,” in ji sanarwar.
Kafin rasuwarsa ya taba buga kwallo a kungiyar Bayern Munich da ke Jamus, inda ya zama abun koyi ga matasan ’yan wasan kungiyar.
Ya taba lashe kyautar Gwarzon Ballon d’Or a shekaru 1972 da 1976, sannan ya yi ritaya daga kwallo a 1984 lokacin da yake murza leda a kungiyar New York Cosmos da ke Amurka.
Tuni duniyar kwallo ta shiga jimami da ta’aziyyar fitaccen dan kwallon duniyar.