Dubban mutane ne suka halarci jana’izar shahararren malamin addinin Musuluncin nan kuma Babban Limamin Masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi da ke Bauchi, Sheikh Dokta Idris Abdulaziz.
Malamin ya rasu ne a ranar Alhamis a gidansa da ke Bauchi bayan fama da doguwar rashin lafiya.
- Kotun ƙoli ta sauke Julius Abure daga shugabancin jam’iyyar LP
- Batun na yanke jiki na faɗi ƙarya ce — Wike
Ya je ƙasashen Masar da Saudiyya domin neman magani kafin watan Ramadan.
Tun da safiyar ranar Juma’a, ɗaruruwan ɗalibansa da mabiyansa daga Bauchi, maƙwabtan garuruwa da kuma wasu jihohi sun taru a gidansa domin halartar jana’izarsa.
An gudanar da sallar jana’izar a ranar Juma’a a filin Idi na Games Village.
Manyan malamai, ’yan siyasa, ’yan uwa da abokan arziƙi da kuma mazauna birnin Bauchi sun halarci jana’izar.
Aminiya ta ruwaito cewar lokaci na ƙarshe da aka gan shi a bainar jama’a shi ne a ranar Sallah, inda ya yi wa al’ummar Musulmi jawabi bayan sallar Idi, inda ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da juna.
Ga hotunan yadda jana’izar ta gudana: