✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon dan kwallon Brazil Romario ya zama Sanata

An zaben da aka gudanar a kasar Brazil a ranar Lahadin da ta gabata, an zabi tsohon dan kwallon Brazil mai suna Romario a matsayin…

An zaben da aka gudanar a kasar Brazil a ranar Lahadin da ta gabata, an zabi tsohon dan kwallon Brazil mai suna Romario a matsayin Sanata bayan ya lashe zaben da kashi 63.4 bisa dari. Zai wakilci yankin Rio de Janaiero ne a majalisar dokokin kasar.
Tsohon dan kwallon ya doke abokin takararsa dan jam’iyyar Democratic mai suna Cesar Maia, bayan Ceasar  ya samu kashi 20.5 na yawan kuri’un da aka kada.
Romario ya zura kwallaye fiye da dubu a lokacin da ya yi kwallo a kulob da dama da suka hada da basco de Gama a Brazil da  PSb Eindhoben da ke Holand da FC Barcelona da balencia na Sifen.
Yana daga cikin ’yan kwallon da suka lashewa Brazil gasar cin kofin duniya a shekarar 1994.
Bayan ya daina kwallo ne ya shiga harkokin siyasa gadan-gadan.  Yana daga cikin masu neman kare hakkin talakawa al’amarin da ya sanya shi karbuwa kuma aka zabe shi Sanata.