Tsohon Alkalin Alkalai, Mai Shari’a Idris Legbo Kutigi ya rasu jiya Lahadi a London bayan wata gajeruwar rashin lafiya da ya yi, ya rasu ne yana da shekara 78.
Biyu daga cikin ‘ya’yansa tsohon dan majalisar wakilan tarayyar Najeriya Sanni Idris Kutigi da kuma Jibrin Musa Kutigi sun tabbatar da mutuwar mahaifinsu.
Allah Ya gafarta masa (Amin)