Ana yawan samun cece-kuce a kan yadda ake yawan samun katardar naira da suka lalace kuma suke da datti a fadin Najeriya. Yawancin takardun kudin da ake amfani da su wajen harkokin kasuwanci sun yage kuma sun yi datti. Idan abokanan hulda suka je bankuna domin a canja musu kudi da suka yi datti a basu masu kyau, yawancin lokaci ba a canja musu mafi yawan bankuna, inda suke cewa babu da sabbin kudi.
Yawancin bankuna suma suna yawan bayar da tsofaffin kudi ne idan aka je cirewa a cikin banki. Rahoton da Babban Bankin Najeriya ya fitar na kukucin da za a rika cirewa idan aka kawo tsofaffin kudi domin a canja musu da sabbi shi ma ya kara bata lamarin. Wani jami’in banki ya ce Babban Bankin na cire kashi biyar na tsofaffin kudin da aka kawo domin a canja da sabbi. Ya ce wannan ne ya sa yawancin banki ba sa son karban tsofaffin kudin daga abokanan huldarsu.
Wani jami’in bankin shi kuma ya ce abin da ya sa ake karancin sabbin kudin shi ne yadda Babban Bankin ba ya buga sabbin kudin akai-akai kamar yadda ya kamata. Amma kuma daraktan hulda da jama’a na Babban Bankin Najeriya na riko, Isaac Okoroafo ya ce, “ba gaskiya bane. Muna buga takardun kananan kudi. Yadda mutane suke wasa da takardun kudi da kuma kasance takardar Naira 100 yana zagayawa da yawa ne suka taimaka wajen lalacewa da yagewar takardun kananan kudi.”
Uzurin da bankuna ke bayarwa ne cewa zuba takardun kudi da suke yi injunan bayar da kuda na ATM ne ya sa takardun kudin suke karanci bai da tushe. Idan har kamar yadda suka ce, kudi mara kyau na bata injin bayar da kudin, wadannan kudaden dai sune suke kawo matsala tsakanin ‘yan kasuwa da abokanan huldarsu. ‘Yan kasuwa da ba sa karban tsofaffin kudi, ana barinsu ne da kayansu ba tare da an saya ba domin masu saya suna dama su zabi shagon da za su sayi abin da suke so. Hakanan kuma suma masu sayan suke tayar da kayar baya idan aka basu irin wadannan kudi a matsayin canji. Haka kuma suma direbobin mashin da motar bas ko yaran mota ke kin karban tsofaffin kudi. Don haka kudaden da ba su da kyau suna da wahalar mu’amala tsakanin mutane kamar yadda suke bata injinunan bayar da kudi. Kodai harkalar saya da sayarwar ta cigaban zamani aka yi ko akasin haka, ya kamata a samu sabbin takardun kudi da yawa.
Ana zargin yawancin bankusa da boye sabbin takardun kudi, inda suka sayar wa ga wasu ejan na bankin da suke sayar da sabbin takardun kudin domin a samu riba. Rafar sabbin naira 100 wanda ya kunshi naira 10,000, ana sayar da shi a kan naira 11,000, musamman ga mutane da suke da biki. Rafar naira 200 kuma wanda ya kunshi naira 20,000, sai a sayar naira 22,000.
Wasu gungun mutane da suka hada da ma’aikatan banki da ejan dinsu ne suka wannan harkallar mara kyau na kasuwancin takardun kudi. Muna kira ga Babban Banki da Hukumar ‘yan sanda su dakile wannan mummunar harkallar, amma kuma muna kiransu da su buga sabbin kudi domin su maye gurbin tsofaffin da ake amfani da su.
Babban matsalar da ake samu wajen janyewa da sake dawo da tsofaffin kudi ita ce matsalar rashawar da ta dabaibaye harkar bata kudin. Rahotanni sun nuna cewa idan aka fitar da kudin za a bata daga Babban Bankin aka ba wasu jami’an bankin a karkashin babban dan sanda, da yawa daga cikin kudin sai su kare a cikin aljihun wadanda aka ba alhakin bata su. Ana zargin cewa wannan matsalar bai canja ba duk da cewa an saka kwamishinan ‘yan sanda ya ci gaba da lura da harkar. Wannan ne ya sa tsofaffin kudi suke dawowa a ci gaba da amfani da su.
Idan ana so a batar da tsofaffin kudi, ya kamata Babban Bankin Najeriya ya yi amfani da dokar da Majalisar Wakilai ta bayar, inda a watan jiya ta umarci Babban Bankin ya daina neman riba ga bankunan da suka dawo da tsofaffin kudi. Wannan tara da Babban Bankin ke karba shi ne dalilin da ya sa bankunan suke kin janye tsofaffin kudi. Hakanan kuma, muna kira ga Babban Banki da ya zabi daya daga cikin mataimakin darakta ya ci gaba da lura da aikin bata tsofaffin kudin.