Bayan kammala zaben shugabannin babbar jam’iyyar hammaya ta PDP hankula sun karkata a kan jam’iyya mai mulki ta APC, domin ganin yadda nata zaben shugabannin zai kaya.
Hakan ba ya rasa nasaba da rikicin da ya barke a wasu jihohi bayan zabubbukan shugabanni da Jam’iyyar APC ta gudanar kamar yadda aka gani a jihohin Kano da Zamfara da Kwara da sauransu.
- Ya auri mata 9 a lokaci guda don nuna musu soyayya
- Camfe-camfe guda 50 da Hausawa suka yi amanna da su
Sai dai a yayin da jam’iyyar take fama da matsalolin da suka faru sakamakon zaben cikin gida, a gefe guda kuma wadansu manyan ’yan siyasa sun soma fafutikar ganin sun samu shugabancinta a matakin kasa.
Kawo yanzu dai mutanen da aka fi jin amonsu sun hada da wadansu tsofaffin gwamnoni hudu wadanda suka fito daga Arewa.
Hakan yana da alaka da hasashen da wadansu ’ya’yan jam’iyyar da masana harkokin siyasa suke yi cewa dan takarar Shugaban Kasar na APC zai fito ne daga Kudu.
Masu nazari kan harkokin siyasa suna ganin cewa, APC na bukatar kwararre kuma gogagge kuma jajirtaccen shugaba domin dinke barakar da ta taso a jam’iyyar.
Tsofaffin gwamnonin da suke son haye kujerar shugabancin jam’iyyar sun hada da tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Abdul’aziz Yari Abubakar da Sanata George Akume, tsohon Gwamnan Jihar Benuwai da kuma Alhaji Umaru Tanko Al-Makura, tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa.
Takaitaccen nazari kan ’yan takarar:
Alhaji Abdul’aziz Yari Abubakar
Alhaji Abdul’aziz Abubakar Yari, mai shekara 53, gogaggen dan siyasa ne, wanda sau biyu yana Gwamnan Jihar Zamfara. Ya kuma taba rike Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, kafin nan ya taba rike Shugaban Jam’iyyar ANPP a Jihar Zamfara.
Bayan kammala wa’adin mulkinsa na Gwamna, Alhaji Abdul’aziz Yari ya yi takarar Sanata a zaben shekarar 2019 kuma ya ci, amma rikicin cikin-gida na jam’iyyarsu ta APC ya sa Kotun Koli ta rusa zaben ta bai wa PDP nasara.
Sai dai Alhaji Abdul’aziz Yari ya ci gaba da taka rawa a jam’iyyar.
Sanata Ali Modu Sheriff Sanata
Ali Modu Sheriff fitaccen dan siyasa ne da ya yi Gwamnan Jihar Borno har sau biyu.
Yana da shekara 66 a duniya. Modu Sheriff ya rike mukaman siyasa da dama. Tun a Jamhuriya ta Uku Sanata Modu Sherrif ya yi Sanatan Borno ta Tsakiya a karkashin Jam’iyyar UNCP lokacin mulkin Sani Abacha.
A 1999 lokacin Jamhuriya ta Hudu an kara zabarsa a wannan mukami a karkashin Jam’iyyar APP.
A 2003, an zabi Modu Sherrif a matsayin Gwamnan Jihar Borno a karkashin ANPP, kuma an sake zabensa a 2007.
Fitaccen dan siyasar ya sha sauya jam’iyya – ya fara siyasarsa a karkashin Jam’iyyar APP/ANPP a wannan zubin siyasa, amma da gamayyar wasu jam’iyyu da suka hada da CPC da ACN da ANPP suka dunkule suka kafa APC shi ma ya koma cikinta a shekarar 2014.
Sai kuma ya koma PDP har zuwa shekarar 2018, inda a PDP ya rike mukamin Shugaban Kwamitin Zaben Shugabannin Jam’iyyar a 2016.
Ya samu kansa a cikin tirka-tirkar shugabancin Jam’iyyar PDP a 2017, sai dai daga bisani Kotun Daukaka Kara da ke Jihar Ribas ta kore shi daga shugabancin jam’iyyar.
Sanata George Akume Sanata George Akume babban dan siyasa ne daga Jihar Benuwai, yana da shekara 67.
Yanzu haka shi ne Ministan Ayyuka na Musamman da Hulda a Tsakanin Bangarorin Gwamnati.
Ya rike matsayin Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Dattawa a 2011 zuwa da 2015.
An zabe shi a Sanata mai wakiltar Benuwai ta Arewa maso Yamma a 2011 har zuwa 2015 da aka kara zabarsa, amma a 2019 sai ya sha kashi a hannun dan takarar Jam’iyyar APC.
Gabanin haka a 1999 lokacin da aka fara Jamhuriya ta Hudu, ya fito takarar Gwamnan Jihar Benuwai kuma ya yi nasara, inda ya kwashe shekara takwas a kan mulki.
Bayan ya fadi zabe ne Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi Ministan Ayyuka na Musamman.
Sanata Tanko Al-Makura Sanata Umaru Tanko Al-Makura tsohon dan gwagwarmayar siyasa ne domin tun a 1980 ya rike matsayin Shugaban Matasan Jam’iyyar NPN a tsohuwar Jihar Filato.
Bayan haka, ya rike mukamai da dama na siyasa da wakilci. Yana cikin jiga-jigan da suka kafa Jam’iyyar PDP a 1998.
Ya zama Gwamnan Jihar Nasarawa har sau biyu, inda aka zabe shi a 2011 a karkashin Jam’iyyar CPC daga bisani CPC ta dunkule a cikin jam’iyyun da suka kafa APC, kuma ya ci gaba da jan zarensa a cikin jam’iyyar.
Masana harkokin siyasa suna ganin za a fafata sosai wajen zaben Shugaban Jam’iyyar APC, kuma da alama an kama hanyar zaben bayan da Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar kuma Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Bagudu, ya sanar da cewa a watan Fabrairun badi za a gudanar da Babban Taron Jam’iyyar.