Ya jama’a! Ku sani, lallai Allah Ya umarce mu da tsayar da adalci a bayan kasa, kuma Ya sanar da mu cewa, da adalci ne sama da kasa suka tsayu. Kuma shi ne ginshiki da tushen samun zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a cikin al’umma. Sannan nagartattun malamai, salihan bayin Allah, irin su Sheihul Islam Ibn Taimiyya da Sheikh Usman Dan Fodiyo da Malam Abdullahin Gwandu sun shaida mana cewa:
“Allah Yana taimakon daular da ta tsayar da adalci koda kafira ce, a yayin da Allah Yake durkusar da daular da take zalunci koda Musulmi ke shugabancin ta.”
Allah Madaukaki Ya umarci Musulmi su tsai da adalci a kowane hali, inda Ya ce:
“Ya ku wadanda suka yi imani! Ku kasance masu tsayin daka domin Allah, masu shaida da adalci. Kuma kada kiyayya da wadansu mutane ta dauke ku a kan ba za ku yi adalci ba. Ku yi adalci shi ne mafi kusa da takawa.”
Kuma Allah Ya ce:
“Kuma idan kun fadi magana to ku yi adalci, kuma koda ya kasance ma’abaucin zumunta ne….”
Kuma Allah Ya sake cewa:
“Lallai Allah Yana muku umarni da adalci da kuma kyautatawa…”
Kuma Allah Ya ce:
“Hakika mun aiko ManzanninMu da hujjoji bayyanannu, kuma Mun saukar musu da littafi da ma’auni domin mutane su tsayar da adalci tsakaninsu…”
Kuma Allah Ya fada a Hadisil Kudusi cewa:
“Na haramta zalunci ga kaiNa, kuma Na sanya shi ya zama haramun a tsakaninku, saboda haka kada ku zalunci junanku.”
Adalci shi ne, bai wa kowa hakkinsa da shari’a ta tabbatar masa, ba tare da nuna kowane irin bambanci ba. Kuma duk inda ake tsayar da adalci, to lallai za a samu zaman lafiya, son juna, walwala, ci gaba da jin dadi a cikin al’umma da tsakankanin jama’a sun yawaita. A Musulunci, tsayar da adalci yana daga cikin manyan kyawawan dabi’u. Wannan ya nuna ke nan duk inda Musulmi suke, indai har Musulmin gaskiya ne, to za a same su sun rungumi adalci.
Kuma Alkur’ani Mai girma ya bayyana karara cewa, Allah Ya umarci mutane da dukan al’ummomi masu neman zaman lafiya da ci gaba, su mu’amalanci juna da kyakkyawar mu’amala, tausayi da tsayar da adalci a duk halin da suka samu kansu a ciki. Kuma kowa yana sane da cewa, Allah Yana son adalci, kuma Ya ki jinin zalunci, kuma ba ya son azzalumai.
Allah Ya wajabta wa dukan mutane, su yi kokari wurin ganin cewa an tabbatar da adalci a bayan kasa, domin samun zaman lafiya mai dorewa. Shi ya sa Allah Ya aiko annabawa, kuma Ya hado su da dokoki, domin su taimaka wa mutane wurin tsayar da adalci. Wahayin da suka karba daga Allah ya nuna hanyar da za a bi a tsayar da adalci a cikin al’umma. Misali, yi wa talakawa adalci, maza da mata, kai hatta makiya an umarce mu da yi musu adalci.
Wajibi ne Musulmi su hada kai domin su dakatar da rashin adalci da zalunci a cikin al’umma. Wannan aiki ne da Allah Ya dora musu. Abu ne da bai dace ba Musulmi su zuba ido, su rungume hannuwansu, suna kallo ana tafka zalunci da rashin adalci ba tare da sun dauki matakin da ya dace wurin tsayar da shi ba.
Aiki da dokokin Allah da shari’arSa wajibi ne a wurin dukan Musulmi. Duk Musulmi ya san cewa siyasa ta kasu kashi-kashi, akwai siyasar Musulunci akwai wadda ba ta Musulunci ba. Misali, siyasar dimokuradiyya ai ba tamu ba ce mu Musulmi. Domin a Musulunci muna da tamu siyasa, wato ta shari’a. Kawai mun samu kanmu cikin wani yanayi ne mu Musulmin Najeriya. Sai aka wayi gari muna yin siyasar dimokuradiyyah a bisa lalura. Wannan tsari na dimokuradiyya, bakon tsari ne a Musulunci da muka amince mu yi shi a bisa lalura. Ke nan ya zama wajibi in dai har muna son zaman lafiya mai dorewa a tsakankaninmu, mu yi wannan tsari a bisa dokokinsa da tsarinsa da masu shi suka tsara shi a kai, na ganin cewa duk wanda ya ci zabe a ba shi. Wanda Allah Ya ba shi a ba shi, kada a yi wa kowa kwace da nuna fin karfi! Domin matukar aka kauce wa wannan, to lallai za mu jefa kanmu cikin tashin hankali, fitina da rudani. Allah Ya kiyaye, amin.
Bari in tambaye mu don Allah, shin yanzu abubuwan da suka gudana a wannan kasa tamu mai albarka Najeriya, na zaben da aka gudanar na gwamnonin jihohi, akwai niyyar tabbatar wa wadansu adalci kuwa? Amsa ita ce: ga alamu, a’a.
Shin me ya sa dukan jihohin da aka ce zabe bai kammala ba, jihohi ne da ake ganin jam’iyyar adawa ta PDP take kan gaba? Shin me ake shirin yi a nan? Shin ana son a murde musu ne? Shin ana da niyyar tabbatar da adalci a wannan al’amari? Amsa dai ita ce: ba mu ga alamun haka ba!
To wallahi, muna kira da babbar murya, ku ji tsoron Allah, kada ku jefa mu cikin rikici da tashin hankali! Don Allah duk wanda Allah Ya ba mulki ku ba shi, kada ku ce za ku murde, ku hana masa. Ku yi wa kowa adalci. Wannan shi zai sa mu samu zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.
Ina mai girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari? Kada ka yi shiru a kan wannan al’amari, ka sa baki don Allah, ka nuna musu duk wanda Allah Ya bai wa a ba shi. Ka tuna fa, kirarinka shi ne MAI GASKIYA. Kada ka bari wadansu miyagu su bata maka tafiyarka. Yi kokari yadda ka fara lafiya ka gama lafiya! Kada ka yarda a danne hakkin wadansu. Ka sani, Allah Yana kallonka, sannan duniya tana kallonka!
Ina Kwamitin Zaman Lafiya na su mai girma tsohon Shugaban Kasa Abdulsalam Abubakar da Mai alfarma Sarkin Musulmi da Rabaran Matthew Hasan Kukah da John Onaiyekan? Ya kamata ku sa baki a cikin wannan al’amari, ku tabbatar cewa duk wanda ya ci zabe an ba shi, domin tabbatar da zaman lafiya a kasarmu mai albarka, Najeriya.
Ina sarakunanmu suke? Ku ne iyayen al’umma, ya zama wajibi ku ba da gudunmawarku wurin ganin an kauce wa tashin hankali. Duk wanda Allah Ya sa ya ci zabe a ba shi hakkinsa.
Ina malamanmu na Musulunci? Shin kun manta da umarnin Allah na tsayar da adalci ne?
Ina fastoci suke? Shin ina zancen tabbatar da adalci da kuke karantawa a littafinku?
Duniya fa tana kallon abin da ke faruwa a Najeriya! Kuma dukanmu muna sane da illar da rashin adalci yake haifar wa mara dadi. Don Allah mu hadu mu yi wani abu a kai.
Irin abin da muke gani da abubuwan da suke faruwa, yanzu dai babu wata dimokuradiyya a Najeriya. Misali:
- A Jihar Kano an ce zabe bai kammala ba, saboda Jam’iyyar PDP ta adawa ce ke kan gaba!
- A Jihar Sakkwato an ce zabe bai kammala ba, a nan ma PDP ce ke kan gaba!
- A Jihar Filato ma an ce zabe bai kammala ba, nan ma PDP ce ke kan gaba!
- A Jihar Adamawa an ce zabe bai kammala ba, nan ma PDP ce ke kan gaba da kuri’u mafiya rinjaye!
- A Jihar Bauchi an ce zabe bai kammala ba, nan ma don sun ga PDP ce ke kan gaba!
- A Jihar Benuwai ma haka, sun ce zabe bai kammala ba, saboda Jihar PDP ce!
- Haka abin yake a Jihar Ribas, an dakatar da duk wasu harkokin zabe, saboda Jihar PDP ce!
Amma wani abin mamaki:
- A Jihar Kaduna an ce zabe ya kammala, saboda APC ce ta yi nasara!
- A Jihar Neja zabe ya kammala, saboda APC ta yi nasara!
- A Jihar Kebbi, zabe ya kammala, saboda APC ce ta yi nasara!
- A Jihar Katsina, nan ma zabe ya kammala, saboda APC ce ta lashe zaben!
- A Jihar Gombe, zabe ya kammala, saboda APC ta yi nasara!
- A Jihar Jigawa, zabe ya kammala, nan ma saboda APC ce ta ci!
- A Jihar Nasarawa, zabe ya kammala, saboda APC ce ta yi nasara!
- A Jihar Kwara, zabe ya kammala, saboda APC ce ta yi nasara!
- A Jihar Borno, an yi kammalallen zabe, domin APC ce ta cinye!
- A Jihar Yobe, nan ma babu matsala, domin ta APC ce!
- A Jihata Zamfara ma an yi kammalallen zabe, saboda jam’iyya mai mulki ta APC ta ci zabe!
Yanzu don Allah za ku gaya mini cewa, wannan abin gaskiya aka bi wurin tabbatar da shi? To in dai har kun yarda, ni kam wallahi, sam ban amince ba.
Maganar gaskiya wannan sharri ne da magudi da rashin adalci irin na ’yan siyasa. Kuma wadannan ’yan siyasa da ke kokarin tafka rashin adalci, wallahi, ba sa son zaman lafiyar al’ummarsu, musamman ma Arewa. Suna son su jefa mu cikin wani sabon tashin hankali da rikici. Allah Ya tsare, amin.
Don Allah me ya sa ne duk inda Jam’iyyar APC ta lashe zabe suka sanar da cinye zaben, amma kuma duk inda Jam’iyyar PDP ke kan gaba suka ce wai ba a kammala zabe ba?
Kuma wai a haka ne za a gaya muna wai ana yin dimokuradiyya. Wace dimokuradiyyar ke nan? Dimokuradiyya ko dai yaudara?
Wallahi bai kamata ku rika wahalar da jama’a ba, matukar kun san kama-karya da rashin adalci za ku yi. Yanzu don Allah abin da ya faru a Kano ba abin kunya ba ne? A ce irin wadannan mutane su ne suke jagorantar al’umma Musulma irin Kano?
Muna addu’a Allah Ya ceto yankinmu na Arewa da Najeriya baki daya, daga sharrin da wadannan mutane ke kokarin jefa su, amin.
Dan uwanku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jihar Kogi.
Imel:[email protected] Tarho: 08038289761.