✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsawa ta kashe mutum 27 a Indiya

Tsawa da guguwa sun yi ajalin mutane akalla 27 tare da raunata wasu.

Akalla mutum 27 ne suka riga mu gidan gaskiya bayan tsawa ta fado musu a Yammacin Jihar Bengal ta kasar Indiya.

Tsawar da aka yi tare da guguwa a yammacin ranar Litinin sun yi barna a yankuna shida na Jihar, inda mutum 27 suka rasu, a cewar Ofishin Kula da Yanayi na kasar.

  1. KASU: Shin an rufe Jami’ar Kaduna saboda karin kudi?
  2. Janar din soja 29 za su tafi hutun barin aiki

Kakakin ’yan sandan jihar, Mrinal Kanti ya tabbatar da cewa tsawa ce ta yi sanadin mutuwar mutum shida.

Wasu daga cikin mamatan da wadanda suka jikkata sun gamu da tsautsayin ne bayan fadowar bishiyoyi da bukkoki da guguwar ta kayar.

Firaminista Narendra Modi, ya bayyana kaduwarsa tare da jaje ga wadanda suka rasu ko suka yi asarar dukiyoyinsu.

Ya ba wa iyalan mamatan kyautar kudi Rupee 200,000, wadanda suka samu rauni kuma Rupee 50,000.

A wani iftila’i da ya faru a babban birnin Jihar Kolkata kuma, tsawa ta kashe fasinja takwas tare da raunata wasu.

Tsawa mai hade da iska mai karfi ta zama ruwan dare a duk lokacin da yanayin damina ya kama a kasar ta Indiya.

Ofishin Kula da Yanayi na kasar ya yi hasashen samun hadura nan gaba cikin yanayin daminar da kasar ta shiga.