✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsawa ta kashe mutum 21 a Indiya

Galibin wadanda suka mutu manoma ne da ke aiki a gonakinsu

Akalla mutum 21 sun mutu bayan wata tsawa da aka yi lokacin da aka shafe sama da awa 24 ana tafka ruwan sama a jihar Bihar da ke Gabashin kasar Indiya.

Wani jami’i a Hukumar Kiyaye Aukuwar Bala’o’i ta Kasar, a ranar Talata ya ce galibin wadanda suka mutun manoma ne da ke aikin shuka a gonakinsu lokacin da lamarin ya faru.

A cewarsa, an sami rahoton mace-macen a gundumomi kusan 10 na jihar.

A garuruwan Purnia da Araria mutum hurhudu sun mutu, uku a Supaul, biyu a Banka da Jamui da Nawada, sai kuma mutum dai-daya a garuruwan Begusarai da Sheikhpura da Saran da kuma Saharsa, inji jami’in.

Babban Ministan jihar ta Bihar, Nitish Kumar, ya sanar da biyan diyyar Rufi 400,000 (kudin Indiya), kwatankwacin Dalar Amurka 5,023 ga dukkan iyalan wadanda iftila’in ya shafa.

Ministan ya kuma shawarci jama’a da su rika yin taka-tsan-tsan da yanayin da ake ciki na damina saboda kaucewa barazanar tsawar.

“Ya zama wajibi mutane su rika bin umarnin da hukumar kula da hasashen ta jiha ke bayarwa don kiyaye kansu daga barazanar tsawar.

“Dole mutane su rika tsaya a cikin gidajensu lokacin da ake ruwan sama,” inji Ministan.