Tsawa ta kaseh wasu mutum uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne domin neman kudin fansa a garin Oro Ago da ke Karamar Hukumar Ifelodun ta Jihar Kwara.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne ranar Litinin.
- Tinubu na son majalisa ta sahale masa kashe biliyan 500 na rage radadin cire tallafi
- Majalisar Wakilai ta nemi a soke ƙarin kuɗin jami’a
A cikin wani bidiyo mai tsawon dakika 30, wanda ya karade kafafen sada zumunta, an ga gawarwakin mutanen su uku sun kone kurmus ba a iya gane su, ga kudaje kuma suna bin su.
Wata murya kuma a kan bidiyon na cewa, “Mu ne ’yan kwamitin bijilan na Igbomina. Kokarin da muke yi na yaki da batagarin da ke aikata ayyukan masha’a a wannan yankin ya fara haifar da da mai ido.
“Tsawa ta kashe wasu da ake zargin masu garkuwa ne su uku. Allah zai ci gaba da taimakon mu a kan duk masu nufinmu da sharri a yankinmu,” in ji muryar.
Mazauna yankin dai sun yi zargin cewa wadanda suka mutun suna cikin wani ayarin masu garkuwa su takwas da suka kai hari yankin Iwo da ke Karamar Hukumar Isin, mako biyu da suka gabata.
A yayi harin na wancan lokacin dai, an kashe wani basarake sannan, sannan aka sace wani jagoran Kiristoci na yankin.
Wani dan kungiyar ci gaban garin Oro-Ago da ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa Allah ne Ya kai tsawar domin ta tallafa musu, amma babu hannun wani mutum a ciki.
Shi kuwa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Ebunoluwarotimi Adelesi, ya ce tuni jami’ansa sun fara bincike a kan lamarin.
Sai dai ya ce ba za su iya tantance asalin abin da ya haddasa tsawar ba, sai nan gaba.