Rahotanni sun bayyana cewa tsawa ta yi ajalin wani limami mai suna Malam Abu Yusuf ɗan shekara 70 a garin Abocho da ke Ƙaramar Hukumar Dekina a Jihar Kogi.
Wani mazaunin garin na Abocho, Dantsoho Sulaiman ya bayyana cewa marigayin limamin unguwar Angwa ne a garin, kuma yana cikin ƙoshin lafiya kafin faruwar lamarin.
“Limamin da ke garin Abocho, wanda ɗan uwansa na kusa ya kira ni ya sanar da ni mutuwar wanda abin ya rutsa da shi.
“An yi ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a garin Abocho da rana har zuwa yammacin yau, yana waje sai ga tsawa wacce ake zargin ita ta kashe shi.
- ’Ya’yana 4 da almajirai 5 sun rasu a gobarar tankar man Jigawa
- Kisan Hanifah: Abdulmalik ya ƙalubalanci hukuncin kisan da aka yanke masa
- NAJERIYA A YAU: Fashewar Tankar Mai: Asarar Da Al’ummar Majiya Suka Tafka
“Ya faɗi ya mutu nan take, hakan bai taɓa faruwa ba a unguwar Abocho, amma a shekarun da suka gabata mun taɓa samun labarin faruwar irin wannan lamari a garin Anyigba, har zuwa rasuwarsa, marigayin shi ne limamin unguwar Angwar ne a garin,” in ji Suleiman.
Mun samu rahoton ne a lokacin da ake ci gaba da shirye-shiryen jana’izar limamin a unguwar.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:40 na yammacin ranar Alhamis a yayin da aka yi ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a unguwar.
Mazauna yankin sun bayyana cewa tsawar da aka yi babu zato babu tsammani ta jefa yankin cikin firgici da makoki.