Wasu giwaye 18 sun mutu bayan da tsawa ta fada musu a yankin Assam Biju na kasar Indiya.
Mutuwar giwayen a ranar Alhamis ta bar baya da kura, inda masana ke zargin lauje cikin nadi, wasu mahukunta kuma na ganin mutuwar Allah da Annabi ce dabbobin suka yi.
- Kwastam sun kashe mutum 5 a garin kama shinkafa
- Janar Dogonyaro: Buhari na alhinin mutuwar sojan da ya yi jawabin yi masa juyin mulki
Jami’an gandun dabbobin da wani dan majalisar Assam, Jitu Goswami, sun ce sun yi amannar tsawa ce ta kashe dabbobin, amma amma wani fitaccen masanin gandun dabbobi a kasar, Soumyadeep Datta, na zargin guba aka sanya musu.
“Ba mamaki guba ce ta kashe su, saboda haka a jira sai an kammala bincike kan mutuwar tasu, wanda nan gaba kadan hukumar kula da gandun daji za ta fitar,” inji shi.
Ya ce hotunan mutuwar dabbobin a wani gandun dabbobin da ke Arewa maso Gabashin kasar, wadanda ake yadawa a kafafen sada zumunta sun nuna akwai alamar tambaya a mutuwarsu.
Tuni dai mahukunta a Indiya sun kaddamar da bincike kan mutuwar giwayen 18 a ranar Juma’a inda suka tura kwararrru tare da Ministan Muhalli na yankin Assam, Parimal Shuklabaidya, domin gano hakikalin lamarin.
Indiya na da akalla giwaye 30,000, wanda shi ne kusan kashi 60% na dabbobin a nahiyar Asiya.
A baya-bayan nan, an samu karuwar rahotannin mazauna na kashe giwaye, kuma giwaye na kashe mutanen da ke yi musu kutse a cikin dazuka.