Wani karamin yaro ya rasu bayan da tsawa ta fada masa a yayin da ake ruwan sama da iska mai karfi.
Tsawar ta fada wa yaron wanda yake aji 1 na Karamar Sakandare ne a yayin da ake buga wasan kwallon kafa.
- Ganduje da Dantata sun sasanta Dangote da BUA
- Kayan shaye-shaye ya kashe mutum 10, wasu 500 na asibiti a Kano
- Yadda matasa ke rububin neman auren ’yar a-mutun Kwankwaso
Ana cikin haka ne sai kwallon ya fita daga fili, shi kuma ya je ya dauko ta, a nan ne tsawar ta fada masa, ta kashe shi.
Lamarin ya faru ne a unguwar Imiringi da ke Karamar Hukumar Ogbia ta Jihar Bayelsa, ranar Alhamis.
Aminiya ta tuntubi kakakin ’yan sandan jihar, SP Asimin Butswat, amma ya ce ba su da labari.